Babban bankin Najeriya CBN
Babban Bankin Najeriya, CBN ya sake kara kudin ruwa a kasar daga 25.750 zuwa 26.25 bayan dakatar da biyan harajin tsaron yanar gizo da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
A Najeriya, darajar Naira ta sake yin sama inda ta karu da kusan N28 a jiya Litinin 20 ga watan Mayu a kasuwannin gwamnati inda hakan ke nuna karuwarta da 1.89%.
Rundunar 'yan sanda a jihar Niger ta yi nasara kan bata garin da ke musanyawa mutanen katin cirar kudi na ATM. Suna dauke da katunan ATM 42 lokacin kamensu.
Tsohon ministan ministan tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi hamdaLah bayan babban bankin Najeriya ya janye harajin tsaron yanar gizo.
‘Dan kwangila ya tona yadda ya ba da cin hancin $600, 00 a lokacin Godwin Emefiele. Victor Onyejiuwa ya kashe $600, 000 (kusan N300m) kafin hakkokinsa su fito a CBN.
Yayin da ƙimar Naira ke kara taɓarɓarewa a kasuwar musaya, jigon PDP ya gano cewa gwamnan CBN, Yemi Cardoso da ministan kuɗi, Wale Edun ne asalin matsalar.
Babbar kotun tarayya mai zama a Maitama a Abuja ta amince da ba da belin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele bayan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa.
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bisa zargin badakala. Bayan sauraron karar, kotun ta bada belinsa a yau.
Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta samar da kwarya-kwaryan kasafi matukar za ta biya karin albashin ma’aikata da kungiyoyin kwadago ke ta fafutukar a yi.
Babban bankin Najeriya CBN
Samu kari