Sanatan PDP Ya Dau Zafi Kan Yadda CBN Ya Kori Ma’aikata 317, Majalisa Za Ta Yi Bincike

Sanatan PDP Ya Dau Zafi Kan Yadda CBN Ya Kori Ma’aikata 317, Majalisa Za Ta Yi Bincike

  • An nemi majalisar dattawa da ta gudanar da cikakken bincike kan yadda babban bankin Najeriya (CBN) ya kori ma'aikata 317
  • Sanata Ned Nwoko (PDP - Delta ta Arewa), ya soki korar da aka yi wa ma’aikatan yana mai zargin an yi rufa-rufa a lamarin
  • An ruwaito cewa tsakanin 15 ga Maris zuwa 24 ga Mayu, CBN ya sallami ma’aikata 317, "ba tare da bayyana dalilin korar ba"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata Ned Nwoko (PDP - Delta ta Arewa), ya soki korar da aka yi wa ma’aikatan bankin CBN su 317 a kwanakin baya.

Sanata Nwoko ya kuma bukaci majalisar dattawa da ta gudanar da bincike kan wannan "dambarwar."

Kara karanta wannan

Daraktoci da manyan ma'aikata sama da 300 sun rasa aikinsu a babban banki CBN

Sanata Ned Nwoko ya yi magana kan dakatar da ma'aikatan CBN
Sanata Ned Nwoko na so majalisa ta binciki yadda aka kori ma'aikatan CBN. Hoto: @Prince_NedNwoko
Asali: Facebook

Dan majalisar dattawan ya shaida wa kamfanin labaran Najeriya (NAN) a ranar Talata a Abuja cewa CBN "ya yi garaje" wajen korar ma'aikatan, don haka akwai bukatar a yi bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai rufa-rufa a korar ma'aikatan CBN" - Nwako

Ya yi zargin cewa babban bankin ya yi rufa-rufa wajen aiwatar da korar kuma bai tuntubi masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyoyin kwadago ba.

Jaridar The Punch ta ruwaito Sanata Nwoko na cewa:

“Ya kamata majalisar dattawa ta umarci kwamitocinta masu kula da ayyukan yi, kwadago da kuma na al’amuran da suka shafi ma’aikatan gwamnati, su binciki korar da CBN ta yi
"Ya kamata kwamitocin su mayar da hankali kan dalilin da ya sa aka yi korar, sanin dokar da aka yi amfani da ita, da kuma tasirin korar ga tattalin arzikin jama'a."

Kara karanta wannan

Notcoin: Dan Najeriya ya samu Naira miliyan 9 daga haƙar ma'adanan crypto a wayarsa

"CBN bai bayyana dalilin korar ba" - Nwako

Kamar yadda kuma jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Sanata Nwoko ya kara da cewa:

“Tsakanin 15 ga Maris zuwa 11 ga Afrilu, 2024, bankin CBN ya kori ma’aikata 117. A ranar 24 ga Mayu, CBN ya sallami karin ma’aikata 200, wanda adadin ya kai 317.
"Daga binciken da na gudanar, babu wani bayani na dalilin kora, ko wani bayani a cikin wasikun kora da aka mikawa ma'aikatan da abin ya shafa."

Kano: Abba ya kori shugaban ARTV

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya dakatar da shugaban gidan talabijin mallakin jihar, ARTV, Mustapha Indabawa.

Bayan dakatar da Indabawa, Gwamna Yusuf ya amince da nadin Hajiya Hauwa Ibrahim a matsayin shugabar ARTV, kuma za ta kama aiki nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel