Bayan Fiye da Shekara 3, Tinubu Ya Tuna Dalilin da Ya Sa Ya Nemi Zama Shugaban Kasa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ganawarsa da mambobin kungiyoyin matasa ta tuna masa dalilin da ya sa ya nemi shugabancin Najeriya
- Tinubu ya gode wa matasan bisa goyon bayansu, jajircewa da imanin da suke da shi na ganin Najeriya ta samu ci gaba
- Shugaban kasar ya yaba wa matasan bisa tsayawa tare da shi a lokutan kalubale da yada sakonninsa a sassa daban-daban na kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ganawarsa da kungiyoyin City Boy Movement, Relax Tinubu Is Fixing Nigeria da sauransu ta tuna masa dalilin da ya sa ya nemi shugabancin kasar nan
Ya nuna godiyarsa ga matasan bisa goyon bayan da suke ba shi, yana mai cewa kuzarinsu, jarumta, jajircewa da imanin da suke da shi na ganin Najeriya ta zama kasa mai ci gaba sun kara karfafa kudurinsa na gina kasar da za ta cika burinsu.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X bayan ganawarsa da mambobin kungiyoyin matasa, wadanda suka taru daga sassa daban-daban na kasar.
Yadda matasa suka tuna wa Tinubu
Shugaban kasar ya ce ganin matasa maza da mata sun taru domin nuna goyon baya ga gwamnatinsa ya tuna masa da makomar da Najeriya za ta iya ginawa ta hanyar kokarin hadin gwiwa.
"Lokacin da na shiga zauren taro jiya, na ga matasa maza da mata na kungiyoyin City Boy Movement, Relax, Tinubu Is Fixing Nigeria da sauran kun yoyin matasa da suka taru, na ga wani abu da ya tuna min dalilin da ya sa na nemi shugabancin wannan babbar kasa," in ji shi.
Shugaban kasar ya kara da cewa, "Na ga Najeriya. Na ga kuzarinta, jarumtarta, jajircewarta da kuma makomar da muke kokarin ginawa tare."
Tinubu ya yabawa matasa
Tinubu ya yaba wa matasan bisa tsayawa tare da shi a lokutan kalubale, kare akidunsu da kuma kai sakonninsa ga al'ummomi a sassa daban-daban na kasar.
A cewarsa, ci gaba da imanin da matasan ke da shi na ganin Najeriya ta zama kasa mai ci gaba ya nuna muhimmancin da suke da shi wajen gina makomar kasar.
Tinubu ya kuma nuna godiyarsa bisa goyon bayan da suke ba shi, inda ya amince cewa ba koyaushe yake samun damar nuna musu godiyarsa kai tsaye ba.
"Akwai wasu kalmomi da ba na yawan furtawa yadda ya kamata, kuma jiya na so ku ji su kai tsaye daga gare ni.
"Na gode.. Na gode da kuka yi imani da ni. Na gode da tsayawa tare da ni," in ji shi.

Source: Facebook
Shugaban kasar ya sake jaddada kudurinsa na gina Najeriya da ta cancanci amincewa, sadaukarwa da burin matasa.
"Zan ci gaba da jajircewa wajen gina Najeriya da ta cancanci imaninku, sadaukarwarku da burinku. Tare, za mu samar da makomar da kuka cancanta da ita," in ji shi.
Bola Tinubu ya yabi dansa Seyi
Kun ji cewa Shugaba Bola hmed Tinubu ya yaba wa dansa Seyi Tinubu kan ayyukansa a kungiyar City Boy Movement a Najeriya.
Shugaban kasar ya ce yana alfahari da yadda Seyi ke hada matasa wuri guda, duk da cewa bai nemi wani mukamin siyasa ba.
Asali: Legit.ng


