Ana Ta Korafi da INEC Ta Nada Matar Mai Tallar Tinubu Ta Zama Darektar Harkar Zabe

Ana Ta Korafi da INEC Ta Nada Matar Mai Tallar Tinubu Ta Zama Darektar Harkar Zabe

  • An nada matar mai magana da yawun Bola Tinubu, Oluyemi Adeyemi-Showunmi, a matsayin shugabar ayyukan zabe a INEC
  • Wannan sauye-sauye na jan hankali da kawo korafi daga manyan 'yan siyasa kamar Atiku Abubakar da ‘yan kafafen sada zumunta
  • Hukumar zabe ta INEC ta yi shiru game da korafin da ake yi, ana fargabar cewa sauyin na iya shafar aminci da gaskiyar zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Nadin Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi da aka yi a INEC ya jawo wa hukumar zabe ta kasa surutan mutane.

Hukumar INEC ta zabi Yemi Adeyemi-Showunmi a matsayin Darektar harkokin gudanar da zabe gabanin takarar 2027.

Zabe.
Wata mata tana kada kuri'a lokacin zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Titilayo Adeyemi-Showunmi ta zama darektar zabe a INEC

Daily Trust ta ce abin da ya fi jan hankalin jama’a shi ne kasancewar sabuwar darektar mai dakin Segun Showunmi a hedikwata.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shirya kayar da Tinubu a jihohi 12 a zaben shugaban ƙasa na 2027

Shi kuwa Segun Showunmi tsohon kakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar ne da yanzu da alama ya canza gidan siyasa.

Mista Showunmi yana tare da APC a yanzu kuma yana cikin kwamitin da ke taya Bola Ahmed Tinubu yakin zaben shugaban kasa.

Matar Showunmi ta canji Isah Gunmi a INEC

Rahotanni sun ce INEC ta dauke Isah Magaji Gummi daga harkar gudanar da zabe, ta maida shi wajen rajistar masu zabe.

Ita kuma Adeyemi-Showunmi da ke bangaren gudanarwa a Legas, ta koma hedikwatar hukumar zaben da yake birnin Abuja.

A karkashin sabuwar darektan ne za a yi duk harkokin zabe tun daga tsare-tsare, shirye-shirye zuwa aika kayayyaki a ranar zabe.

Titilayo Adeyemi-Showunmi ce kuma za ta kula da sha’anin ma’aikatan da za a tura wuraren aikin zabe.

Atiku Abubakar ya ankarar da mutane

Phrank Shaibu wanda Darekta ne wajen yakin neman zaben Atiku Abubakar ya fara ankarar da jama’a kan canjin da aka yi.

Kara karanta wannan

Wajen rantsar da kwamitin kamfe ya zama matattarar habaici tsakanin Akpabio, Wike da gwamnoni

Baya ga Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi, kakakin Atiku Abubakar ya ce an nada Dr Lawrence Bayode ya jagoranci sashen ICT.

A cewar Shaibu, wadannan wurare su ne zuciyar harkar shirya zbe, don haka ya ce dole a fadi dalilin sauye-sauyen da INEC ta yi.

Jama'a sun nemi INEC ta yi wa duniya bayani

Duk da ba ita ce ta ke da wuka da nama wajen bada nasara ba, akwai masu ganin nadin nata zai iya yin tasiri a takarar badi.

Wannan ya sa irinsu Chidi Odinkalu suke ta korafi musamman a X, suna cewa da alamar akwai lauje cikin nadi a lamarin INEC.

Leadership ta rahoto HURIWA tana neman shugaban INEC, Joash Amupitan ya yi bayanin hikimar sauye-sauyen da ya yi.

HURIWA ta bakin Kwamred Emmanuel Nnadozie Onwubiko ta jefa alamar tambaya game da nadin da shugaban hukumar INEC ya yi.

Duk da kiran da ake ta yi, har zuwa yanzu hukumar INEC ba ta cewa duniya komai ba tukuna.

NDC ta maido wa INEC aiki baya

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

Rahoto ya zo cewa an bar NDC babu ‘dan takaran gwamna a Bauchi a sa’ilin da aka cire sunan wadanda ta tsaida a Kano da Kaduna.

Ana shirin kamfe Ibrahim Kashim Abdullahi ya sanar da shugabannin jam’iyyar NDC a Bauchi cewa ya yi murabus a ranar 16 ga Oktoba 2026.

Tun a Mayun 2026 ya sayi fom ɗin takarar gwamna sai yanzu ake samun labari ya rabu da jam’iyyar NDC mai adawa lokacin da aka soma kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng