An Shirya Hallaka Atiku Ana Shirin Zaben 2027? Kwamitin Kamfen APC Ya Magantu

An Shirya Hallaka Atiku Ana Shirin Zaben 2027? Kwamitin Kamfen APC Ya Magantu

  • Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya musanta zargin cewa akwai shirin kashe Atiku Abubakar, yana mai cewa jami’an tsaronsa suna nan
  • APC ta buƙaci Timi Frank ya gabatar da hujjoji kan zargin, tare da kira ga hukumomin tsaro su gayyace shi domin gudanar da bincike
  • Timi Frank ya nemi Donald Trump da sauran shugabannin ƙasashen duniya su sa baki kan zargin yunƙurin tsoratarwa da kama Atiku yayin yaƙin neman zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

ABUJA: Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC-PCC) ya bayyana cewa babu wani shirin kashe tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Kwamitin ya dage cewa ba a janye jami’an tsaron da aka ware wa Atiku ba.

Kara karanta wannan

Sanata Tambuwal na shirin ficewa daga ADC zuwa APC? An ji yadda zancen yake

Ya ce zargin da Timi Frank, wani mamba na ADC, ya yi ƙarya ne, kuma dole ne ya gabatar da hujjoji don tabbatar da shi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Dele Alake, ya ce:

“Mun yi watsi da zargin cewa fadar shugaban ƙasa ta Najeriya ko kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na da hannu a duk wani shiri na kashe tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ko wani ɗan adawa.”

Sanarwar ta ce, “Wannan babban zargi ne da dole Mista Frank ya tabbatar. Saboda haka, muna kira ga hukumomin tsaro su gayyace shi domin ya gabatar da hujjojinsa, ganin girman zargin da kuma muhimmancin kare rayuka cikin gaggawa.”

Kwamitin ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa an janye jami’an tsaron Atiku.

Ya ce, “Rahoton cewa an janye jami’an tsaron da aka ware wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa ƙarya ce tsagwaronta. Atiku na samun cikakken kariya daga ’yan sanda da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS).”

Ya ƙara da cewa, “Sabanin ƙaryar da Timi Frank ke yaɗawa, Shugaba Tinubu ya bayar da umarni kwanan nan ga hukumomin tsaro su ƙara ƙarfafa kariya ga ’yan takarar shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu a faɗin ƙasar.”

Kara karanta wannan

Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Kwamitin ya ce ba a taɓa yin sakaci da tsaron ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ba.

Ya bayyana cewa, kasancewarsa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku na samun matakan kariya biyu da gwamnati ke ɗaukar nauyinsu.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya ƙara tsaurara tsaron Atiku a matsayinsa na ɗan takarar shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.

Sai dai kwamitin ya ce ba zai yi wasa da duk wata barazana ta gaske ba.

Sanarwar ta ce, “Muna kuma kira ga Mista Frank da kada ya yi jinkirin gabatar da duk wani bayani da yake da shi domin a gudanar da bincike cikin gaggawa. Dole ne a ɗauki duk wata sahihiyar barazana ga rayuwa da muhimmanci, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba.”

Kwamitin ya bayyana zargin a matsayin wata dabara da ’yan adawa suka saba amfani da ita.

Ya ce, “Zargin Mista Frank wata dabara ce ta ’yan adawa ta tayar da hankalin jama’a da kuma ƙara ɗumama siyasa. Da dama daga cikin ’yan adawa, ciki har da Timi Frank, sun mayar da rubuta wasiƙun buɗe ido da sanya shugabannin ƙasashen waje da ƙungiyoyin duniya a saƙonnin kafafen sada zumunta al’ada, domin jawo hankalin da bai dace da su ba.”

Kara karanta wannan

An kai maganar barazana kan rayuwar Atiku gaban Shugaba Trump

Kwamitin ya kuma yi nuni da tarihin Shugaba Bola Tinubu a siyasar adawa.

Alake ya ce, “Shugaba Bola Tinubu, a matsayinsa na dattijo kuma mai kishin dimokuraɗiyya, ya fahimci cewa siyasar adawa muhimmin ɓangare ne na dimokuraɗiyyar Najeriya mai shekaru 27.

“Tinubu ya kasance fuskar adawa a Najeriya tsawon shekaru 16, kuma ya ƙarfafa ƙungiyoyin adawa har suka kayar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a zaɓen 2015.”

Ya ce yayin da yaƙin neman zaɓe ke ƙara ƙarfi, ’yan siyasa da magoya bayansu za su ci gaba da yin maganganu marasa tushe da zarge-zargen da ba su da muhimmanci domin samun ribar siyasa.

Alake ya buƙaci ’yan takara, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su riƙa faɗin gaskiya da yin magana cikin ɗaukar nauyi a bainar jama’a.

Ya ce su guji kalaman da za su iya haddasa tashin hankali da za a iya kauce wa.

Ya ƙara da cewa, “Mu tabbatar gasar siyasa ta kasance cikin lumana, bisa doka, tare da mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi ’yan Najeriya, maimakon ɓata suna ko yin zarge-zargen da ba su da tushe.”

Kara karanta wannan

Abin da ya fi firgita Kashim Shettima kan zaben 2027 fiye da Atiku da Obi

Zargin da Timi Frank ya yi

A nasa ɓangaren, tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC ta ƙasa, Timi Frank, ya yi gargaɗi kan zargin cewa akwai shirin tsoratar da Atiku Abubakar da kuma kama shi ta hannun Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC).

A cikin wata wasiƙa ta buɗe ido da ya aikewa Shugaban Amurka, Donald Trump, da sauran shugabannin ƙasashen duniya, Frank ya nemi sa hannun diflomasiyya kan zargin barazana ga rayuwar tsohon mataimakin shugaban ƙasa da ’yancinsa na siyasa.

Frank, wanda jakada ne mai kula da Gabashin Afirka da Gabas ta Tsakiya a ƙungiyar United Liberation Movement for West Papua (ULMWP), sannan babban mai ba da shawara ga Global Friendship City Association ta Amurka, ya ce zarge-zargen na buƙatar bincike mai zaman kansa cikin gaggawa.

Ya ce, “Dole ne a gudanar da bincike mai zaman kansa kan waɗannan zarge-zarge cikin gaggawa. Saboda girman lamarin, bai kamata a yi watsi da su ko a ƙyale su ba har sai lokacin da zai yi wuya a hana cutarwa.”

Kara karanta wannan

Shin Tinubu ya karya doka da ya ce ba zai je kamfe wasu jihohin Najeriya ba? An samu bayani

Ya bayyana damuwarsa ta musamman kan yiwuwar amfani da EFCC wajen fara shari’a a kan Atiku, ta yadda hakan zai iya kai ga kama shi da tsare shi na dogon lokaci yayin yaƙin neman zaɓe.

Frank ya ce, “Damuwar ba ita ce a ɗauki Atiku Abubakar a matsayin wanda doka ba ta shafa ba. Abin da ya dame mu shi ne kada a taɓa amfani da doka wajen zaluntar abokan hamayyar siyasa.

“Kare ’yan adawa ba wata alfarma ba ce da gwamnati za ta bayar bisa son ranta. Wajibi ne na asali ga kowace ƙasa mai bin tsarin dimokuraɗiyya.”

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.