Kashim Shettima Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Ceto Najeriya daga Sangarcewa

Kashim Shettima Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Ceto Najeriya daga Sangarcewa

Manyan Labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce tattalin arzikin Najeriya da ya riga ya durƙushe idan ba don matakan da Bola Tinubu ya ɗauka ba
  • Shettima ya amince cewa ’yan Najeriya sun sha wahala, amma ya yi hasashen farashin kayan abinci zai ragu nan da makonni masu zuwa saboda sabbin matakan noma
  • Ya ce ajiyar kuɗaɗen waje ta Najeriya ta kusa dala biliyan 60, yayin da tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin ɗari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce tattalin arzikin Najeriya da ya durƙushe idan ba don matakan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka ba.

Shettima ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin masu sukar Tinubu da sun kasance suna rubuta rahotannin durƙushewar tattalin arzikin ƙasar ne daga biranen Dubai da New York.

Kara karanta wannan

Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Shettima ya yaba salon mulkin Tinubu
Kashim Shettima, Shugaba Bola Tinubu da Oluremi Tinubu yayin kaddamar da kwamitin kamfe a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Shettima ya bayyana hakan ne a zauren liyafa na fadar shugaban ƙasa, yayin wani taro da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya, cewar Vanguard.

Shettima ya yaba wa Bola Tinubu

Shettima ya yaba wa shugaban ƙasar bisa hangen nesansa, sannan ya bayyana cewa nan da makonni masu zuwa, Tinubu zai fito da sabbin matakai domin magance ƙalubalen noma, wanda zai taimaka wajen rage farashin kayan abinci.

Yayin amincewa da cewa ’yan Najeriya sun sha wahala, Shettima ya ce halin da ake ciki da ya fi muni idan ba don matakan da Tinubu ya ɗauka ba.

Ya ce:

“Ya kamata a yaba wa shugaban ƙasa, ba a yi masa baƙar magana ba. Eh, ’yan Najeriya sun sha wahala, amma da abin ya fi haka muni. Ku kasance da tabbaci cewa nan da makonni masu zuwa, shugaban ƙasa zai fito da ƙwararan matakai domin magance ƙalubalen noma, kuma farashin kayan abinci zai ragu.”

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce ana ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya, inda ya kawo Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin matakan tallafa wa jama’a.

Ya kuma roƙi matasa da su fita su isar da saƙon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ga sauran ’yan Najeriya.

Kashim Shettima ya ce Tinubu ya ceto Najeriya
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Karfin hali da Shugaba Tinubu ya nuna

A cewarsa, shugaban ƙasar ya nuna ƙarfin hali da cikakken ilimi wajen ɗaukar manyan matakai da suka sauya alkiblar tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin ɗari a zangon ƙarshe da ya gabata, yayin da ajiyar kuɗaɗen waje ta kai kusan dala biliyan 60, cewar Punch.

Shettima ya ce:

“Ku tuna irin nisan da muka yi. Waɗanda suka taɓa kasancewa a cikin kwari mafi zurfi ne za su fahimci girman darajar kasancewa a saman dutse.”

Abba Kabir ya ce Arewa ta Tinubu ce

Mun ba ku labarin cewa Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da goyon bayan Arewa ga burin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Gwamnan ya ce Kano za ta jagoranci sauran jihohin Arewa wajen ƙarfafa fitowar masu kaɗa ƙuri’a ga Tinubu.

Ƙungiyar Arewa for Asiwaju, ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, na son tallata ayyukan Tinubu da tattara goyon baya ga tikitin Tinubu da Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.