Tsohon Mataimakin Sanusi II Ya Yi Kira 1 wajen Taya Shi Murnar Dawowa Karaga

Tsohon Mataimakin Sanusi II Ya Yi Kira 1 wajen Taya Shi Murnar Dawowa Karaga

  • A yau ne gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf za ta mika takardar nadi ga Muhammadu Sanusi II
  • Fitattun mutane a ciki da wajen Najeriya sun fara miƙa sakon taya murna ga sabon sarkin bisa dawo da shi fada da aka yi
  • Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu ya taya Sanusi II murna tare da yin kira na musamman ga gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A yau Jumu'ah ne gwamnatin jihar Kano za ta mika takardar nadi ga mai martaba Muhammadu Sanusi II kan dawo da shi sarautar Kano.

Sanusi
KIngsley Moghalu ya bukaci ba sarakuna kariya. Hoto: Kingsley Moghalu
Asali: Facebook

Yan uwa da abokan arziki sun fara taya Muhammadu Sanusi II murnar nada shi Sarkin Kano na 16 a yau.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun yi magana kan sake maɗa Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu ya taya Sanusi II murna cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi: Sakon da Moghalu ya wallafa

Kingsley Moghalu ya ce yana matukar farinciki da ganin an dawo da Muhammadu Sanusi sarautar jihar Kano.

Ya kuma bayyana Sanusi II a matsayin mai gidansa a lokacin da suke aiki a babban bankin Najeriya.

Moghalu ya ce nadin sarautar ya shiga tarihi da za su dade ba su manta da shi ba a rayuwarsu. Ga abin da yace:

"Ina matukar farin ciki da ganin gwamantin jihar Kano ta gyara kuskuren da aka yi a baya. Ina mika godiya ga gwamna Abba Kabir Yusuf da yan majalisar jihar Kano.
"Lallai sauke mai martaba sarki Muhammadu Sanusi II da aka yi a shekarar 2019 zalunci ne babba"

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Duk da umarnin kotu, Gwamna Abba zai mika takardar nadi ga Sanusi II

- Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu

Moghalu ya yi kira a ba sarakuna kariya

A cikin sakon da Kingsley Moghalu ya wallafa ya yi kira ga gwamnati kan samar da kariya ta musamman ga sarakuna da masarautu.

Ya bukaci a samar da doka a kundin mulkin kasa da za ta hana gwamnonin jihohi cin karensu ba babbaka kan sarakunan gargajiya.

Mahaifiyar Sanusi ta gana da mahaifiyar Abba

A wani rahoton, kun ji cewa mamar Abba Kabir Yusuf tayi zama da mahaifiyar Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II a jihar Kano.

A lokacin da suka gana, tsofaffin sun yi wa jihar Kano addu’o’i, aka kuma roki Allah SWT ya maida Khalifa cikin gidan dabo domin cigaba da mulki kamar yadda ya fara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel