Darajar Naira Ta Kara Sama Yayin da Dala Ta Karye a Kasuwar Musayar Kuɗi a Najeriya

Darajar Naira Ta Kara Sama Yayin da Dala Ta Karye a Kasuwar Musayar Kuɗi a Najeriya

  • Kuɗin Najeriya sun kara daraja a kasuwar hada-hadar musayar kuɗi ta bayan fage ranar Talata, 28 ga watan Mayu, 2024
  • Naira ta ƙara farfaɗowa zuwa N1,500 kan kowace Dalar Amurka ɗaya daga N1,520 da aka yi hada-hada a ranar Litinin da ta gabata
  • Haka nan kuma a kasuwar musaya ta gwamnati, Naira ta yi raga-raga da Dala inda ta tashi zuwa N1,339.33 daga N1,481.23

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Darajar Naira ta ƙara tashi a kasuwar ƴan hada-hadar kuɗi ta bayan fage, inda ta dawo N1,500 kan kowace Dala ranar Talata, 28 ga watan Mayu.

Naira ta ƙasa farfaɗowa a jiya Talata daga N1,520 da aka yi musanyar kuɗin Najeriya kan kowace Dalar Amurka ɗaya a ranar Litinin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Dala: Naira tayi gagarumar galaba mafi girma a cikin watanni 2, ta tashi a kasuwa

Musayar Naira zuwa Dala.
Naira ta kara farfaɗowa a kasuwar ƴan canji da farashin gwamnati a Najeriya Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Har ila yau, ƙimar Naira ta ƙara tashi a kasuwar musayar kuɗi ta gwamnati, ta koma N1,339.33 kan kowace Dalar Amurka ɗaya, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naira ta tashi a farashin gwamnati

Bayanai daga hukumar kula da cinikayyar kuɗi ta ƙasa FMDQ sun nuna cewa farashin Dala ya fadi zuwa N1,339.33 kan kowace dala daga N1,481.23.

Legit Hausa ta fahimce cewa Naira ta farfaɗo da N143.9 lokaci ɗaya a kasuwar musayar kuɗi ta gwamnati a jiya Talata.

Sakamakon haka, tazarar da ke tsakanin farashin Dala a kasuwar gwamnati da farashin kasuwar ƴan canji ya karu zuwa N160.67 daga N43.77 a ranar Litinin.

CBN ya ɗauki matakan gyara Naira

Wannan na zuwa ne yayin da babban bankin Najeriya (CBN) ke ci gaba da ɗaukar matakai da nufin dawo da ƙimar kuɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya

CBN ya ɗauki matakai da dama ciki har da sayar wa ƴan canji dubban Daloli da kuma soke lasisin wasu ƴan canji a Najeriya.

A baya-bayan nan babban bankin ya umarci dukkan ƴan kasuwar musayar kuɗi su sabunta lasisin da suke da shi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

CBN ya kori ɗaruruwan ma'aikata

A wani rahoton kuma CBN ya ƙara korar ma'aikata sama da 300 ciki har da daraktoci, mataimakan daraktoci, manyan manajoji da ƙananan ma'aikata.

Rahotanni sun nuna cewa daga ranar Alhamis zuwa Jumu'a, bankin ya raba gari da daraktoci 14 cikin 17 da suka rage waɗanda suka yi aiki da Emefiele.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262