Kwankwaso na Fuskantar Matsala a Kano, Yan Takarar NDC 5 Sun Dura kan Yan Kwankwasiyya

Kwankwaso na Fuskantar Matsala a Kano, Yan Takarar NDC 5 Sun Dura kan Yan Kwankwasiyya

  • ’Yan takarar Majalisar tarayya biyar na NDC a Kano sun zargi Kwankwasiyya da tsoratar da su kan waɗanda za su wakilci jam’iyyar a zaɓen 2027
  • Sun zargi Kwankwasiyya da cin zarafi da kuma ƙoƙarin matsa wa INEC lamba domin ta sauya sahihin jerin sunayen ’yan takarar jam’iyyar
  • ’Yan takarar sun buƙaci a mutunta hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano na ranar 14 ga Oktoba 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wasu ’yan takarar Majalisar tarayya biyar na NDC a jihar Kano sun zargi tafiyar siyasa ta Kwankwasiyya da tsoratar da su kan waɗanda ya kamata su wakilci jam’iyyar a zaɓen shekara mai zuwa.

’Yan takarar sun kuma zargi Kwankwasiyya da ke cikin NDC da cin zarafi, tare da ƙoƙarin yi wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) baƙar magana domin matsa mata lamba ta sauya sahihin jerin sunayen ’yan takarar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2027: PDP, NDC sun shiga kafar wando da INEC kan cire sunayen yan takararsu

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso tare da yan Kwankwasiyya Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Yan takara 5 sun soki Kwankwasiyya

Tashar Channels tv ta rahoto cewa ’yan takarar sun haɗa da Abdulmajid Umar, mai neman wakiltar mazaɓar tarayya ta Gwale da Shaaban Sharada, mai neman wakiltar mazaɓar tarayya ta Kano Municipal.

Sauran su ne Ismael Sani, mai neman wakiltar mazaɓar tarayya ta Kumbotso; Ibrahim Bango, mai neman wakiltar mazaɓar tarayya ta Sumaila/Takai; da Nasir Ahmed, mai neman wakiltar mazaɓar tarayya ta Nassarawa a jihar Kano.

A cikin ƙorafi mai shafuka bakwai mai kwanan wata 17 ga Oktoba 2026, wanda lauyoyin Bola AIDI, SAN & Co. suka sanya wa hannu, a Kano, ’yan takarar biyar sun soki ƙorafin da Kwankwasiyya ta shigar kwanan nan a gaban INEC.

Dalilin zargin yan Kwankwasiyya a Kano

Maimakon haka, sun buƙaci tafiyar Kwankwasiyya ta mutunta hukuncin Babbar Kotun Tarayya.

A cewarsu ya kamata a mutunta hukuncin da kotu ta yanke a ranar 14 ga Oktoba 2026, wanda ya tabbatar da sahihancin takarar mutum biyu daga cikinsu a matsayin ’yan takarar NDC a Kano, yayin da ta ɗage yanke hukunci kan sauran mutum ukun.

Kara karanta wannan

Yan takarar gwamnan jam'iyyar adawa sun fadi wanda za su yi a zaben shugaban kasa

Sun nuna takaicinsu kan yadda, duk da cika ƙa’idojin doka da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ya sa ska miƙa sunayensu ga INEC, wani babban jigon mai tasiri a NDC a Kano ya kawo cikas ga bin tsarin da ya dace.

Kwankwasiyya.
Taron mabiyar tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano Hoto: Kwankwasiyya Movement
Source: Facebook

’Yan takarar sun jaddada cewa ba za su bari wani a NDC ya sauya sunayen da hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa ta miƙa wa INEC ko ya fifita ra’ayinsa kan hukuncin kotun da ke da hurumin shari’a ba.

Sanarwar ta ce:

“Babban jigon ya bayyana a fili cewa yana da niyyar hana su tsayawa takarar zaɓen 2027 a Kano ƙarƙashin NDC. Zanga-zangar da aka yi kwanan nan a INEC ta shafi waɗannan ’yan takara biyar ne.”

Yan Kwankwasiyya sun yi zanga-zanga

Kun ji cewa magoya bayan Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano, suna neman INEC ta dawo da sunan ɗan takarar gwamnan NDC.

Ɗn takarar mataimakin gwamna na NDC, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa ofishin INEC, inda suka miƙa takardar ƙorafi kan cire sunan Gwarzo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262