Jihar Borno
Yayin da ake fargabar tashin yaƙi idan ECOWAS ta ɗauki matakin soji a kan jamhuriyar Nijar, an tattara jihohin Najeriya Bakwai da suka haɗa iyaka da Nijar.
Ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun sake kai wani mummunan hari a yankin tafkin Chadi, inda suka halaka masunta masu yawan gaske ta hanyar yi musu yankan rago.
Gwamnan jihar Borno ya shirya tallafawa mabuƙata sama da mutum 1.8m a jihar Borno. Gwamnan ya ƙaddamar da sabon rabon tallafi wanda mabuƙata 1.8m za su amfana.
Makonni kaɗan bayan halaka manoma kusan 15, mayaƙan kungiyar ta'addanci watau Boko Haram sun kuma yanke wasu manoma kusan 10 a kauyuka biyu na jihar Borno.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya cire sunan Dr. Ibrahim Yusuf Ngoshe daga cikin jerin wadanda ya ke son nadawa a matsayin kwamishinoninsa.
Gwamnatocin Borno da Yobe da Adamawa sun samar da bas bas a cikin gari don ragewa mutane radadin cire tallafi da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi a watan Mayu.
Gwamna Umara Zulum ya rantsar da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da masu ba shi shawara na musamman. Gwamnan ya kuma rantsarda shugabannin riƙon ƙwarya.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta sanar da kama wasu mata 2 da kuma maza 8 bisa zarginsu da hannu wajen halaka wani jami'in hukumar. Kwamishinan 'yan sandan.
Joy Bishara wacce ta na daya daga cikin 'yan matan Chibok da suka kubuta a hannun 'yan Boko Haram ta samu mijin aure a kasar Amurka bayan kammala digiri a can.
Jihar Borno
Samu kari