Jihar Benue
Hukumar makarantun firamare a jihar Benue (SUBEB) a ranar Juma’a, 6 ga watan Satumba, ta bayyana cewa a shirinta na yin tankade da rairaya ta gano sunayen matattun malamai 256 wadanda har yanzu suna cikin jerin masu karban albashi
Tarihi ya tabbatar da cewa, rikici a tsakanin kabilar Tibi da Jukun ya faro ne tun a shekarar 1959, kuma ya sake faruwa a shekarun 1980, 1990, da kuma na shekarar 2001 gabanin sake faruwarsa a bana.
Ikon Allah sai kallo, kuma dama masu iya magana sun ce idan da raka ka sha kallo, an samu wata karamar yarinya mai shekaru 10 a duniya, Masenengen Targbo da ta haihu a jahar Benuwe, yankin Arewa ta tsakiya, a Najeriya.
Uwargidar Ihongo, Monica Ihongo ta bayyana ma manema labaru cewa yan bindigan sun kwashe musu duk wasu abubuwa masu muhimmanci a gidan, daga nan suka tura maigidanta cikin mota.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Omolulu Bishi ya bayyana haka a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar inda ya taso keyar barayin.
Majiyar Legit.ng ya ruwaito tun a makonni biyu da suka gabata ne rikicin kabilanci ya barke tsakanin kabilun jahohin biyu da suke kan iyaka da juna, kabilar Jukun da Kabilar Tibi, inda zuwa yanzu an kashe akalla mutane 35, tare da
Legit.ng Akalla mutane biyar ne suka mutu a sakamakon wani sabon hari da wasu gungun yan bindiga suka kai zuwa kauyen Mondo dake cikin garin Ukembragya-Gaambetiev na karamar hukumar Logo ta jahar Benuwe, a daren Talata.
Tun da misalin karfe 9 na safe ne magoya baya suka fara taruwa a filin wasan, haka zalika yansanda masu bada hannu akan titi sun yi aiki tukuru don ganin sun magance matsalar cunkoson ababen hawa a yayin ziyarar ta Buhari.
Kaakakin Yansandan jahar, DSP Moses Yamu ne ya bayyana haka, inda yace lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 18 ga watan Oktoba a garin Zaki Biam dake jahar Benuwe, kuma tuni likitoci suka tabbatar da mutuwar mutanen uku.
Jihar Benue
Samu kari