Rikicin jahar Benuwe: Yan ta’adda sun halaka jami’an dansanda da mutane 2 a Zaki Biam

Rikicin jahar Benuwe: Yan ta’adda sun halaka jami’an dansanda da mutane 2 a Zaki Biam

Rundunar Yansandan jahar Benuwe ta bayyana cewa jami’inta guda daya da wasu mutane biyu sun gamu da ajalinsu a yayin wata musayar wuta da aka yi tsakanin Yansanda da kungiyar yan bindiga ta Shitte, yaran rikakke dan ta’adda Gana.

Kaakakin Yansandan jahar, DSP Moses Yamu ne ya bayyana haka, inda yace lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 18 ga watan Oktoba a garin Zaki Biam dake jahar Benuwe, kuma tuni likitoci suka tabbatar da mutuwar mutanen uku.

KU KARANTA: Jama’a ayi hattara: Ba na bada tallafin naira dubu goma goma – Atiku

LEGIT.com ta ruwaito Kaakaki Moses Yamu yana cewa: “Yan ta’addan Shitte sanye da kayan Sojoji ne suka afka cikin garin Zaki Biam akan baburan Bajaj a kokarinsu na tserewa yayin da Sojojin dake aikin kakkabe yan bindiga a Benuwe suka biyo su.

“Nan da nan DPO na Yansandan yankin ya tattara jami’an yansanda suka taru don taran yan bindigan, isarsu garin ke da wuya, sai aka fara musayar wuta, wanda yayi sanadin mutuwar wani jami’in Dansanda sa’annan yan bindigan suka tafi da bindigansa, haka nan fararen hula biyu sun mutu.

“Fararen hulan da suka mutun sun hada da wata mata da karamin yaro, sai kuma mutane biyu da suka samu rauni, wanda a yanzu haka sna samun kulawa a asibitin Light of Grcace dake cikin garin Zaki Biam.” Inji shi.

Shima kwamishinan Yansandan jahar, Ene Okon ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yayi kira ga jama’a da kada su shiga dimuwa, don kuwa jami’an Yansanda na iyakan kokarinsu don tabbatar da tsaro a jahar gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: