Jerin wasu jahohin Arewa da gwamnoninsu suka shiga yawon duniya yayin da ake kashe jama’a

Jerin wasu jahohin Arewa da gwamnoninsu suka shiga yawon duniya yayin da ake kashe jama’a

A yanzu haka da muke tattara wannan rahoto gwamnonin jahohin Taraba da Benuwwe, watau Gwamna Darius Ishaku da Gwamna Samuel Ortom basa Najeriya, sun shilla kasashen waje yawon duniya yayin da jahohinsu ke cigaba da ruruwa daga kashe kashen kabilanci.

Majiyar Legit.ng ya ruwaito tun a makonni biyu da suka gabata ne rikicin kabilanci ya barke tsakanin kabilun jahohin biyu da suke kan iyaka da juna, kabilar Jukun da Kabilar Tibi, inda zuwa yanzu an kashe akalla mutane 35, tare da barnata dimbin dukiya.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da wasu manyan daraktocin hukumar FIRS guda 9

Jerin wasu jahohin Arewa da gwamnoninsu suka shiga yawon duniya yayin da ake kashe jama’a
Ortom da Ishaku
Asali: UGC

Wannan rikici ya faru ne daga kauyen Kente dake cikin karamar hukumar Wukari ta jahar Taraba, inda daga nan yayi naso zuwa karamar hukumar Ukum ta jahar Benuwe, yayin da Tibabe ke ikirarin Jukunawa sun kashe musu mutane 23, su kuma Jukunawa na ikirarin Tibabe sun kashe musu mutane 12.

Da wannan ne jam’iyyar APC reshen jahar Taraba ta bayyana damuwarta game da halin ko-in-kula da gwamnan jahar Darius Ishaku ya nuna game da halin rashin tsaron daya addabi jahar, kamar yadda kaakakinta, Aaron Thomas ya bayyana.

“Abin mamaki ne da takaici ace gwamna sukutum baya nan a daidai lokacin da jaharsa ke ci da wutar rikici, muna da labarin yana kasar Amurka, mun rasa mai gwamnan keyi da kudaden tsaron jahar Taraba tun bayan hawansa gwamna.” Inji Thomas.

Majiyarmu ta ruwaito shi kuma Gwamna Ortom yana hutun shekara shekara ne. amma an samu musayar yawu tsakanin shugaban karamar hukumar Wukari, Daniel Ali da na karamar hukumar Ukum, Iber Logo.

Yayin da Ali ke zargin Logo da masaniya game da maharan Tibabe dake kai musu hari suna kashe musu mutane, amma yaki amincewa ya kamasu, shi kuma Logo zargin Ali yake yi da daukan nauyin matasan Jukun zuwa kauyen Igbogom inda suka bude ma jama’an kauyen wuta yayin da ake zaman sulhu.

Daga bangaren Yansanda kuwa, kaakakin rundunar Yansandan jahar, David Misal ya bayyana cew suna yin iya bakin kokarinsu don shawo kan lamarin, inda ya kara da cewa zasu jagoranci zaman tattaunawa na sulhu tsakanin kabilun biyu a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel