Ruwa baya tsami banza: An kama jami’in Soja cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane

Ruwa baya tsami banza: An kama jami’in Soja cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane

Rundunar Yansandan jahar Benuwe ta sanar da kama wasu gungun gagga gaggan barayin mutane dake yin garkuwa da mutane domin samun kudin fansa, inda tace ta bankado wani korarren jami’in rundunar Sojan Najeriya a cikin miyagun.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Omolulu Bishi ya bayyana haka a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar inda ya taso keyar barayin.

KU KARANTA: Yadda wani Magidanci ya saki matansa 2 a lokaci guda saboda fitina

Ruwa baya tsami banza: An kama jami’in Soja cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane

An kama jami’in Soja cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane
Source: UGC

A jawabinsa, kwamishina Bishi yace sun kama Terngu Ackaa, tsohon jami’in Sojan Najeriya mai mukamin Sajan da aka sallama daga aiki a kwanakin baya, tare da abokin barnarsa, Msugh Ako, bayan samun bayanan sirri game da shirin da suke yi na yin garkuwa da wasu mutane biyu a garin Gboko.

Kwamishinan yace a baya ma sun samu rahoto Ackaa ya taba sace wata mata a jahar Benuwe, har sai da iyalanta suka biyashi naira miliyan goma sha daya a matsayin kudin fansa kafin ya saketa, sa’annan yace gungun yan fashin ne suka addabi yankin Gboko zuwa Katsina Alan a jahar.

Sai dai a wani mataki mai daukan hankali, Sajan Ackaa ya musanta tuhumar da ake masa, inda yace wasu ne suka shirya masa gadar zare da nufin ya fada saboda wata makarkashiya da suke nufinsa da shi, amma bai bayyana sunayensu ba.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Benuwe ta kama akalla mutane goma da zargin aikata laifuka daban daban a jahar, inda yace sun kwato bindigu guda 8, da alburusai 17, babura 4 da kuma mota guda daya.

Daga karshe kwamishinan ya bayyana cewa zasu gurfanar da miyagun mutanen gaban kotu don fuskantar hukuncin daya dace dasu da zarar sun kammala gudanar da bincike akansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel