Manufarmu shine kashe mutane 20 – Madugun mai garkuwa da mutane a Benue

Manufarmu shine kashe mutane 20 – Madugun mai garkuwa da mutane a Benue

Wani dan shekara 30 mai suna Iorwuese Kpila, Shugaban kungiyar wasu fitinannun makasa, masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi da makami, wadanda ke ta’addanci a tsakanin karamar hukumar Ushongo na jihar Benue, a ranar Juma’a, 27 ga watan Satumba ya bayyana cewa wata saraunniyar aljanu ta ba shi da mambobin kungiyarsa aikin kashe mutane 20 sannan su kai jininsu domin ayi tsafi.

Ya bayyana cewa basu yi nasarar cika umurnin da sarauniyar ta basu ba kafin yan sanda suka kama su.

Sai dai ya bayyana cewa sun yi nasarar garkuwa da kuma kashe mutane 16 tare da binne su a cikin rami mai zurfi da ke Gabtse, karamar hukumar Ushongo.

Lorwuese wanda ya bayar da wannan jawabi a lokacin da aka gurfanar dasu a hedkwatar yan sandan jihar Benue da ke Makurdi tare da mambobin kungirsa shida, ya bayyyana cewa yaso ace ya samu karfi da daukaka a garinsa harma a gaba da jihar Benue.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa 'Yan sandan jihar Benue sun gano kaburbura 11 a kauyen Gbatse a karamar hukumar Ushongo inda ake zargin masu garkuwa da mutane sun birne wadanda suka kashe.

KU KARANTA KUMA: An gudanar da sallar Juma’a na musamman domin bikin ranar yanci a Abuja (hotuna)

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, ASP Catherine Anene, ya sanar da manema labarai a Makurdi cewa an kama daya daga cikin wadanda ake zargi, "Ana kammala bincikarsa za a bada cikakken bayani".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel