Gidan gonar mangwaron Obasanjo za ta ba dinbin mutane aiki a Benuwai
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce gidan gonar mangwaronsa da ke Garin Howe a cikin karamar hukumar Gwer da ke jihar Benuwai za ya dauki jama’a da-dama aiki.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, tsohon Shugaban kasar ya bayyana wannan ne a Ranar Litinin, 4 ga Watan Nuwamba, lokacin da ya je wani zagaye a gonar domin duba inda aka kwana.
Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa gidan gonan zai rika samar da lemun da aka yi daga ruwan mangwaro. Bugu da kari, za ayi amfani da kwallon mangwaron wajen yin magunguna.
A yayin da Obasanjo ya je ziyarar kewayen gonar, ya bayyana cewa: “Na zo ne domin abubuwa hudu; na farko in ga yadda gidan gonar ta fara. Sai kuma in godewa gwamna da goyon bayansa.”
KU KARANTA: Wani ya mutu a wajen gasar cin kwai a kasar Indiya
Ba a nan kurum Obasanjo ya tsaya da jawabin na sa ba, inda ya kara da cewa ya zo ne domin “Godewa al’ummar yankin da su ka karbemu, sannan kuma in fadawa ma’aikata abin da za ayi.”
“Ma’aikatan daga wannan yankinsu ke. Mangwaron za su fara fitowa ne nan da shekaru uku ko hudu. Mu na da kusan eka 140 na filin wannan aiki. Za a gina kamfanin sarrafa magwaro a nan.”
“Sama da mutane dubu za a dauka aiki a yayin da aka kammala gina kamfanin. Lemu da mangwaron da mutane su ke nomawa ba za su isa a kafa kamfani ba, shiyasa mu ka bude gona.”
Mai girma gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom wanda ya yi wa Obasanjo rakiya ya tabbatar da cewa a shirye gwamnatinsa ta ke da taimakawa masu wannan tunanin zuba jari a harkar noma.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng