Karamar yarinya yar shekara 10 ta haihu a jahar Benuwe
Ikon Allah sai kallo, kuma dama masu iya magana sun ce idan da raka ka sha kallo, an samu wata karamar yarinya mai shekaru 10 a duniya, Masenengen Targbo da ta haihu a jahar Benuwe, yankin Arewa ta tsakiya, a Najeriya.
KU KARANTA: An yanke hukuncin zaman shekar 5 a kurkuku ga wani Fasto da ya yi ma yarinya fyade
Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito yarinyar ta haihu ne a wani babban asibitin garin Makurdi, kamar yadda wani mutumi mai suna Ukan Kurugh ya tabbatar, wanda yace shi da wasu mutane suka kai yarinyar asibiti.
“Bayan na samu labarin nakudar yarinyar, sai muka tafi da wasu mutane muka tafi babban asibitin gwamnati Makurdi inda muka nemi su bamu izini mu dauketa daga nan, sai muka kai ta asibitin Foundation dake garin Makurdi domin samun isashshen kulawa.
“Da misalin karfe 1 na dare muka dauketa daga babban asibitin gwamnati zuwa asibitin Faoundation, duka duka bai wuce awa daya da kaita asibitin ba Mesenengen ta haihu, inda ta haifi jaririya mace wanda nauyinta ya kai kilo 2:5, bayan an yi mata tiyata.” Inji shi.
Dole ta sanya aka yi ma yarinyar tiyata sakamakon kugunta sun yi kadan ta haihu dasu, don haka ta shiga cikin mawuyacin hali yayin da nakuda ya kamata.
Sai dai har yanzu ba’a san wanene ya dirka ma wannan karamar yarinya ciki ba, sakamakon marainiya ce, kuma fyade aka yi mata a sansanin yan gudun hijira dake jahar Benuwe inda take rayuwa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng