An gano sunayen malamai 256 da suka mutu cikin wadanda ake biyan albashi a hukumar SUBEB na jihar Benue

An gano sunayen malamai 256 da suka mutu cikin wadanda ake biyan albashi a hukumar SUBEB na jihar Benue

Hukumar makarantun firamare a jihar Benue (SUBEB) a ranar Juma’a, 6 ga watan Satumba, ta bayyana cewa a shirinta na yin tankade da rairaya ta gano sunayen matattun malamai 256 wadanda har yanzu suna cikin jerin masu karban albashi.

Shugaban SUBEB, Mathew Mnyam, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Makurdi don bikin cikarsa wata guda a kujerar shugabanci, yace an cire sunayen daga cikin masu karban albashin.

Mnyam ya kuma bayyana cewa daga cikin tsaftace hukumar, an tura daraktoci hudu hutun dole na watanni uku domin ba hukumar damar duba lamura da dama cikin tsanaki.

Ya kara da cewa an dakatar da wani ma’aikaci da ke da alhakin kula da ragamar sunayen da aka kama da sanya wasu sunaye tare da wani ma’aikaci da aka yiwa sauyin waje daga hukumar bayan ya kasa jawabin aikin da aka bashi.

KU KARANTA KUMA: Jihar Niger: Kotun zabe ta jaddada nasarar Sanata Musa

Mnyam yayi barazanar cewa bada dadewa ba hukumar za ta bi ta kan wasu manyan sakatarorin kananan hukumomi da basa kokari yayinda ya gargadi shugabannin makarantu da ke karban kudade daga iyaye kafin kwasan yaransu da su janye daga hakan ko kuma su fuskanci doka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel