Benuwai: Miyetti Allah Kautal Hore ba su gagari hukuma ba - Ortom

Benuwai: Miyetti Allah Kautal Hore ba su gagari hukuma ba - Ortom

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi magana game da barazanar da kungiyar Miyetti Allah Kauta Hore ta ke yi na cewa dole jihohi su bude wuraren kiwon dabbobi ko ayi rikici.

Mai girma Samuel Ortom, ya fitar da jawabi ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai, Mista Terver Akase, inda ya fadawa kungiyar Makiyayan cewa ba su karfin doka ta hau kansu ba.

Wannan jawabi da ya shiga hannun Manema labarai ya na cewa: “Mun karanta wasu bayanai masu tada hankali a jaridu da aka alakanta su da shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore.

Bayanin da CPS ya sa wa hannu ya ce: “…Abdullahi Bodejo ya na barazana ga Gwamnonin da su ka ki kafa wuraren kiwon da ake kira RUGA, idan ba haka ba, ba za a samu zaman lafiya ba.”

“Kalamai irin na Badejo su na iya tada zaune-tsaye kuma fito-na-fito ne kai tsaye da gwamnati. Babu wata kungiya da za ta fi karfin doka, ta na fadawa jihohi yadda su ke so a kan ra’ayin jama’a.”

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tadawa 'Yan makaranta hankali a Zamfara

Ortom ya cigaba da cewa: “Mu na kira a cafke shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na kasa, a kuma gurfanar da shi bisa laifin yawan yin maganganun da za su iya tada rigima."

“Bodejo a kafafen yada labarai ya ware gwamna Ortom wajen ci masa mutunci, ya na cewa gwamnan ya na wasa da hankalin jama’a kan dokar haramta kiwo saboda ya cin ma burin siyasa.”

“Haka kuma ya zargi gwamna Ortom da laifin kashe Fulani Makiyaya tare da kiransa ya fito ya nemi afuwa. Shugaban na Miyetti Allah Kautal Hore ya rantse dokar kiwo ba za ta yi aiki ba.”

“Mu na ganin wannan kalamai ba a matsayin barazana ga zaman lafiya kadai ba, har da yunkurin sake jawo hare-haren ‘yan ta’addan Makiyaya a Garuruwan Benuwai kamar yadda aka yi a baya.”

Kwanakin baya dai kun ji cewa kungiyar ta Miyetti Allah Kautal Hore ta Makiyayan Najeriya ta fito ta ba gwamna Samuel Ortom hakuri a game da kashe-kashen da su ka yi a Arewa ta tsakiya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: