Rundunar 'yan sanda ta kama dan majalisa a APC da hannu dumu-dumu a garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sanda ta yi awon gaba da mamba a majalisar dokokin jihar Benuwe, Honarabul Jonathan Agbiye, zuwa Abuja bayan bayanan sirri sun nuna cewa yana da hannu dumu-dumu a satar mutane domin yin garkuwa da su.
An zabi Honarabul Agbiye ne a matsayin mamba mai wakilta mazabar Katsina-Ala a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
An samu honarabul Agbiye da laifn mallakar wata mota kirar Toyota Hilux wacce rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa mallakar marigayi Jastis Tine Tur ce.
Honarabul Agbiye ya ci zabe babu hamayya a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben shekarar 2019, ba tare da jam'iyyar PDP ta kalubalanci nasarar da ya samu ba.
An alakanta nasarar da honarabul Agbiye ya samu a zaben 2019 da tsoron ubangidansa na siyasa, kasurgumin dan ta'adda, mai garkuwa da mutane, Terwase Akwaza (wanda aka fi sani da 'Gana'), da kowa ke yi.
Rahotanni sun bayyana cewa Gana ya yi barazanar cewa zai kashe duk wanda ya kalubalanci nasarar da honarabul Agbiye ya samu.
Hakan ne yasa dan takarar jam'iyyar PDP bai nufi kotu domin kalubalantar nasarar da honarabul Agbiye ya samu ba.
Wani mutum ne da rundunar 'yan sanda bata bayyana sunansa ba ya aika da takardar korafin neman a binciki honarabul Agbiye, musamman zargin da ake yi na alaka mai karfi a tsakaninsa da Gana.
Rundunar 'yan sanda ta tura jami'ai na musamman daga Abuja domin sa ido a kan mu'amala da harkokin dan majalisar, lamarin da ya kai an same shi da motar sata mallakar tsohon alkali.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng