Tirkashi: An sake gano kabarin sirri a jihar Benue

Tirkashi: An sake gano kabarin sirri a jihar Benue

Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro a jihar Benue a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba sun sake bangado wani kabari da sirri a gari ZakiBiam da ke karamar hukumar Ukum na jihar.

Wannan na zuwa ne makonni uku bayan yan sanda sun gano wasu kabarurruka na mutane da dama da yan kungiyar asiri suka kasha suka binne a karamar hukumar Ushongo.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano rubabben gawar wata mata da ake zargin matar jami’in da sanda ne wacce ta bata tare da mijinta tun a watan Mayun wannan shekarar.

An tattaro cewa ana zargin wasu yan bindiga ne suka kashe jami’in da sandan da ya bata, Sajen Abraham Ihom, da matarsa a gidansu da ke ZakiBam sannan suka dauke su.

An rahoto cewa dan sandan da abun ya shafa na aiki ne a karkashin yan sandan yankin Katsina-Ala sannan cewa ya ziyarci ahlinsa ne a gari ZakiBam da ke makwataka a Ukum lokacin da lamarin ya afku.

Sai dai kuma ba a gano gawar jami’n dan sandan ba a daidai lokacin kawo wanna rahoton.

KU KARANTA KUMA: Ba lafiya: Bidiyon yadda tankar mai ke ci da wuta a hanyar babban titin Lagas-Ibadan

Kakakin yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, wanda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai, ya bayyana cewa an kama wadanda ke da hannu a lamarin sanna cewa an tura su ofishin rundunar yan sandan jihar dake Makurdi.

Anene ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar, Mukkadas Garba, zai yiwa manema labarai jawabi kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel