Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kwalejin kimiyyar lafiya

Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kwalejin kimiyyar lafiya

Shugaban kwalejin kimiyyar kiwon lafiya dake garin Mkar, cikin karamar hukumar Gboko na jahar Benuwe, James Terwase Ihongo ya fada hannun masu garkuwa da mutane, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 1 ga watan Yuli ne yan bindigan suka yi awon gaba da Ihongo a kan hanyar Katsina Ala zuwa Mkar, da misalin karfe 7:30 na dare.

KU KARANTA: Allah Ya tseratar da Magajin garin Daura bayan shafe wata 2 a hannun barayi

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan na biye da Ihongo na tsawon lokaci amma bai sani ba, har sai lokacin da suka daidaici ya shiga gidansa, daga nan suka yi wuf suka daukeshi a cikin wata mota kirar Toyota mai ruwan toka.

Uwargidar Ihongo, Monica Ihongo ta bayyana ma manema labaru cewa yan bindigan sun kwashe musu duk wasu abubuwa masu muhimmanci a gidan, daga nan suka tura maigidanta cikin mota.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar don jin ta bakinta, Catherine Anene, sai tace har yanzu basu samu rahoton garkuwa da shugaban kwalejin ba.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya ta samu nasara ceto magajin garin Daura, Musa Uba daga hannun masu garkuwa da mutane da suka rikeshi na tsawon watanni biyu.

Rundunar tace ta bankado gidan da yan bindigan suke rike da Magajin ne a rukunin gidajen Gangar ruwa dake unguwar Samegu cikin karamar hukumar Kumbotso, zuwa yanzu dai ta kama mutane biyu tare da kwato makamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel