Gungun yan bindiga sun bindige wani babban dan jarida a jahar Benuwe

Gungun yan bindiga sun bindige wani babban dan jarida a jahar Benuwe

Wasu gungun miyagu da ba’a san ko su wanene ba sun bindige wani babban ma’aikacin gidan rediyon Najeriya, FRCN, Harvest FM, Injiniya Patrick Kumbul a garin Makurdi na jahar Benuwe, tare da diyar makwabcinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kumbul, wanda shi ne shugaban sashin kimiyya da fasaha na gidan rediyon Harvest FM Makurdi ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindigan ne a kofar gidansa dake titin Daniel Amokachi da misalin karfe 8 na dare.

KU KARANTA: Zuwa daya: Jami’an EFCC sun nade shuwagabannin kananan hukumomi 16 a jahar Kwara

Kaakakin Yansandan jahar Benuwe, Catherine Anene ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace yan bindigen sun halaka Kumbul ne a daren Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, sai dai tace a yanzu haka suna bin sawun yan bindiga.

Bayanan da majiyarmu ta tattaro shi ne yan bindigan guda 6 sun bi sawun Kumbul ne a kan babura har zuwa gidansa yayin da suke sanye da kayan sarki na jami’an tsaro, isarsu gidansa ke da wuya suka bude masa wuta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun kashe Kumbul ne a lokacin da yake kokarin neman sanin su wanene su. Zuwa yanzu dai gwamnan jahar Benuwe, Samuel Ortom ya nemi Yansanda su yi duk mai yiwuwa wajen kama miyagun.

Gwamnan ta bakinsa, Terver Akase ya yi kira ga jama’an garin Makurdi dasu taimaka ma jami’an tsaro da bayanan sirri masu amfani da zasu taimaka musu wajen kama miyagun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: