Buhari ya nemi a kawo karshen rikicin Tibi da Jukun

Buhari ya nemi a kawo karshen rikicin Tibi da Jukun

Bayan da ya sha matsin lamba, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nemi gwamnonin jihar Taraba da Benuwe da su gaggauta kawo karshen rikicin kabilanci da ke ci gaba da aukuwa karo bayan karo a tsakanin Tibi da Jukun.

Babba shakka wannan dadadden rikici wata tsohuwar gaba ce da ke ci gaba da janyo asarar rayuwa gami da salwantar dukiya baya gaba sauran kalubale na ta'addanci da kasar ke ci gaba da fuskanta musamman musamman musibar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, rikicin makiyaya da manoma, hare-haren 'yan bindiga da kuma ta'adar masu garkuwa da mutane.

Muryar Duniya ta ruwaito cewa, umarnin shugaba Buhari na zuwa a daidai lokacin da sabuntar rikicin a tsakanin kabilun biyu ya yi kamari, inda a ranar Larabar makon da ya gabata aka yi wa wani babban Limamin Addinin Kirista na darikar Katolika, Rabaran David Tanko kisan gilla.

Ana zargin wasu gungun mahara da kawowa yanzu ba a tantance ko su wanene ba suka yi wa jagoran mabiyar addinin kiristan kwanton-bauna a kauyen Kufai Amadu da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba, inda suke kone gawarsa da kuma motarsa kurmus.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasa, shugaban Buhari ya nemi sarakunan gargajiya na kabilun Tibi da Jukun, da shugabanni addini, da shugabannin al'ummomin jihar Taraba da Benuwai, da su aiwatar da zaman sulhu domin kawo karshen wannan rikici da ya zame masu annoba.

Hakazalika shugaban kasar ya ce ci gaba ba zai taba samuwa ba a yankin matukar tababa ta rikici za ta ci gaba zame wa al'ummomin biyu karfen kafa.

Tarihi ya tabbatar da cewa, rikici a tsakanin kabilar Tibi da Jukun ya faro ne tun a shekarar 1959, kuma ya sake faruwa a shekarun 1980, 1990, da kuma na shekarar 2001 gabanin sake faruwarsa a bana.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, akalla gidaje 300 aka babbake a ranar Asabar ta makon da ya shude yayin sabunta rikici a tsakanin kabilar Jukun da Tibi a jihar Taraba, inda ake zargin tsagerun kabilar Jukun ke da alhakin kai wannan mummunan hari.

Wannan mummunan hari ya jefa dubunnan mutane cikin halin ni 'ya su a sanadiyar salwantar muhallansu kamar yadda wani mai ba da shaida ya labartawa manema labarai na jaridar The Nation.

Sai dai bayan aukuwar harin na baya-bayan nan, wani uban gayya na kabilar Tibi, Stephen Butu, ya yi kira ga al'ummarsa a kan su zauna lafiya tare da daukar dangana inda ya yi neman kada su mayar da martani.

Babu shakka a halin yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza samun sukuni yayin da aka huro masa wuta a kan tabbatar da kawo karshen rikicin da ke tsakanin kabilun Jikun da kuma Tibi a jihar Taraba.

A wata zanga-zanga da aka gudanar cikin Abuja a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, wasu 'yan asalin jihar Taraba da kuma wadanda lamarin ke ciwa tuwo a kwarya, sun nemi shugaban kasa Buhari da ya shiga tsakanin rikicin da ya janyo asarar rayukan mutane da dama tsawon shekaru aru-aru.

Cikin wata rubutacciyar wasika zuwa ga shugaba Buhari da sa hannun madugun masu zanga-zangar, Mike Msuaan da kuma Solomon Adodo, sun roki gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta dauki mataki a kan masu haifar da fitina da rashin zaman lafiyar al'umma a jihar Taraba.

KARANTA KUMA: Diyyar $9.6bn: Osinbajo ya jagoranci zaman 'yan majalisar tattalin arziki

Masu zanga-zangar sun bayar da shaidar cewa, a halin yanzu su kansu kabilun Tibi da Jukun sun kosa wajen ganin sulhu ya tabbata a tsakaninsu wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sun kuma nemi shugaban kasa Buhari da ya umarci dukkanin hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki wajen bankado masu hura wutar rikicin da ke tsakanin kabilun biyu wanda ya ki ci ya ki cinyewa tsawon shekaru bila adadin.

Daruruwan rayuka dai sun salwanta tare da asarar dukiya mai tarin yawa ta biliyoyin nairori a sanadiyar wannan mummunan rikici da ke ci gaba da aukuwa a tsakanin kabilun Jukun da Tibi tsawon shekaru aru-aru.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel