Kuma dai: An sake kashe mutane 5 a wani hari da yan bindiga suka kai jahar Benuwe
Akalla mutane biyar ne suka mutu a sakamakon wani sabon hari da wasu gungun yan bindiga suka kai zuwa kauyen Mondo dake cikin garin Ukembragya-Gaambetiev na karamar hukumar Logo ta jahar Benuwe, a daren Talata.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun banka wuta a wasu kauyukan dake makwabtaka da kauyen Mondo, akan iyakokin jahar Benuwe da jahar Taraba da kuma jahar Nasarawa.
KU KARANTA: Anyi batakashi tsakanin Yansanda da masu garkuwa da mutane a cikin garin Kaduna
Wani shugaba a karamar hukumar Logo, Cif Joseph Anawah ya bayyana cewa sun samu labarin wasu gungun mahara da suke kyautata zaton yan bindiga ne sun fara haurowa yankinsu ta cikin ruwa, kwatsam sai gashi yan bindigan sun kai hari a kauyen Mondo suka kashe mutane biyar.
Mutanen da suka kashe sun hada da Torkaa Gbim, Celina Tavershima, Ayilaga Tavershima, Sonter Tavershima da Terkaa Tavershima, sa’annan akwai wasu kuma da har yanzu babu wanda masaniyar halin da suke ciki ko kuma inda suke.
Shima shugaban karamar hukumar Logo, Richard Nyajo ya shaida ma majiyarmu cewa tabbas yan bindiga sun kai wannan hari a Mondo, kuma sun kashe mutane biyar tare da jikkata wasu mutane biyu.
Tuni dai karamar hukumar ta kai koke zuwa ga kwamandan rundunar Soji dake yaki da yan bindiga a jahar Benuwe, Manjo Janar Adeyemi Yekini, sai dai babban Sojan yace banu hannun Fulani makiyaya a wannan hari, inda yace harin ya samu asali ne daga rikicin kabilun Jukun da Tibabe.
“Sojojina sun ziyarci kauyen da aka kai harin, kuma sun tabbatar da harin ya samo asali ne daga cikin kabilun Tibabe da Jukun da ya barke a ranar Talata a kauyen Kente na jahar Taraba ne, kuma nayi magana da mashawarcin Gwamna Samuel Ortom akan harkar tsaro, inda ya kama hanya zuwa Taraba don sasanci tsakanin bangarorin dake fadan.” Inji shi.
Shima shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jahar Benuwe, Haruna Ibi ya bayyana cewa bashi da masaniyar rikici tsakanin jama’ansa Fulani makiyaya da yan kauyen, ya kara da cewa wannan rikici ne tsakanin Jukunawa da Tibabe.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng