Yerima Ya Ce Yarinya Yar Shekara 14 da Ya Aura Yanzu Tana Karatun Digiri Na 2

Yerima Ya Ce Yarinya Yar Shekara 14 da Ya Aura Yanzu Tana Karatun Digiri Na 2

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima, ya yi karin bayani game da amarya yar shekara 14 da ake zargin ya aura a 2010
  • Yerima ya bayyana cewa a yanzun yarinyar ta girma kuma tana kan matakin karatun digiri na biyu a jami'a
  • Ya caccaki wasu dokokin kare hakkin ɗan adam a Najeriya inda ya ce ba zasu zama doka ba sai majalisun jiha sun yi karatu a kansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara State - Sanata Ahmed Sani Yerima ya kare kansa dangane da auren yarinya 'yar shekara 14 'yar asalin ƙasar Masar a shekarun da su shuɗe.

Idan baku manta ba, wannan aure ya haddasa cece kuce kuma ya tada ƙura a sassan Najeriya da kuma duniya baki ɗaya shekaru 13 da suka gabata.

Ahmad Sani Yeriman Bakura.
Yerima Ya Ce Yarinya Yar Shekara 14 da Ya Aura Yanzu Tana Karatun Digiri Na 2 Hoto: channels
Asali: Facebook

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi ca kan tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Yerima, bayan labari ya karaɗe ko ina a 2010 cewa an ɗaura masa aure da yarinya wacce ake zargin shekarunta 13 kacal.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

Auren wanda aka ɗaura da babban masallacin kasa Abuja ya jawo dole majalisar dattawa ta gudanar da bincike saboda a lokacin Sanata Yerima na cikin mambobinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan ya faɗi asalin shekarunta da halin da take ciki yanzu

A halin yanzun, Sanata Ahmed Yerim, wanda ya bayyana a shirin siyasa a yau na kafar Channels tv, ya ce Amaryarsa da aka yi ta cece ku ce a baya ta girma.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa a yanzun wannan Amarya da ya aura tana karatun digiri na biyu a jami'a.

Sai dai ya musanta cewa shekarunta 13 a wancan lokaci da aka ɗaura musu aure amma da aka tambaye shi ko ta kai shekara 15 a lokacin, ya ce, "Tsakanin nan dai, 14 zuwa 15."

Sanata Yerima ya caccaki wasu kundin dokokin kare haƙƙin dan adam 2003 da 2005, inda ya ƙara da cewa duk dokar da majalisar tarayya ta zartar sai majalisun jihohi sun yi duba a ciki sun amince.

Kara karanta wannan

Ahmad Gumi Ya Yi Bayani Kan Ainihin Dalilan Tinubu 2 Na Yi Wa Sama Da Sojoji 100 Ritayar Dole

"Kuma idan har ba su yi nazari a kai ba, ba ta zama halastacciyar doka ba," inji shi.

Talauci da Jahilci Ne Suka Haddasa Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Sani Yerima

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima, ya ce talauci da jahilci ne ya haifar da ayyukan ta'addancin 'yan bindiga.

Sanata Ahmed Sani Yerima ya ce idan ka kalli duk masu hannu a lamarin, zaka ga talauci da jahilci ne suka jefa su ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel