Arewa
Mau garkuwa da mutane sun sace wasu 'yan mata 23 da wasu ma'aikatan kamfanin yin hanya 10 a harin da suka kai a jihar Zamfara a ranar Laraba 26 ga watan Yuli.
Niger - Rahotanni sun tabbatar da cewa an gano jaririn da wata mata ta ɗauke daga shagon mahifiyarsa a kasuwae Minna, babban birnin Neja cikin koshin lafiya.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da buƙatar shugaban ƙasa, A.Bola Ahmed Tinubu, ta naɗa mutane 10 a hukumar raya shiyyar arewa maso Gabashin Najeriya.
Kotun majistare da ke zamanta a jihar Kano ta tasa keyar wasu mutane 25 gidan kaso kan zargin mallakar takardun bogi na Hukumar Kula da Dokokin Hanya ta KAROTA.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Suke ya bayyana yadda Aliko Dangote ya masa halacci tare da ba shi shawarar neman gwamna da kuma daukar dawainiyarshi a jihar.
Jami'an tsaro sun kwamushe wasu mutane hudu da ake zargin shirya kai hari gidan tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar a Yola da kuma wasu wurare a birnin Yola.
Wasu tsagerun yan daba sun bi dare sun ƙone ofishin yakin neman zaben jam'iyyar SDP da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi, sun lalata muhimman kayan aiki.
Rahotanni daga jihar Kogi sun bayyana cewa rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a yankin ƙaramar hukumar Yagba da gabas, kuma an rasa rayuka da dama.
Masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun yi barazanar auren 'yan mata hudu da ke hannunsu idan har iyayensu ba su biya kudin fansa N12m nan da mako daya ba.
Arewa
Samu kari