Yadda Dangote Ya Bani Shawarar Neman Gwamna Da Kuma Daukar Nauyi Na, Gwamna Sule Ya Yi Bayani

Yadda Dangote Ya Bani Shawarar Neman Gwamna Da Kuma Daukar Nauyi Na, Gwamna Sule Ya Yi Bayani

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana yadda Dangote ya masa kara a rayuwarsa
  • Gwamna Sule ya bayyana yadda Alhaji Aliko Dangote ya ba shi shawara ya nemi gwamna tare da daukar nauyin shi
  • Ya ce bai taba ganin mai saukin kai irin Aliko Dangote ba duba da yadda ya ke da arziki amma bai dauki hakan komai ba

Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana irin goma ta arziki da Alhaji Aliko Dangote ya yi masa a rayuwarsa.

Gwamnan ya ce ba zai taba manta irin halaccin da Dangote ya masa ba tare da nuna masa goyon baya a rayuwarsa.

Gwamna ya bayyana irin saukin kai na Aliko Dangote da kuma abin da shawarar da ya ba shi
Gwamna Sule Ya Yi Tsokaci Kan Abubuwan Da Aliko Dangote Ya Yi Masa A Rayuwa. Hoto: Global Times.
Asali: Facebook

Sule ya bayyana haka ne yayin wata hira da DCL Hausa a ofishinsa da ke Lafia cikin jihar.

Yadda Dangote ya ba shi shawarar neman gwamna a Nasarawa

Kara karanta wannan

Rikita-rikita Yayin Da Mata Ta Haifi 'Yan 4 Bayan Mijin Ya Yi Niyyar Zubar Da Cikin, Ya Nemi Taimako

Ya bayyana cewa Aliko Dangote ne ya bashi shawarar ya nemi gwamna kuma ya dauki nauyin shi har karshe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bai taba ganin mutum mai saukin kai irin Dangote ba ganin yadda ya ke da kan-kan da kai a mu'amalarsa da mutane.

A cewarsa:

"Abu na farko da ba zan mantaba shi ne saukin kan Dangote.
"Lokaci ina darakta a Kamfanin Mai na Afirka (African Petroleum) kafin ma na fara aiki da shi, ya zo da kudinsa da komai ya yarda ya zama daga cikin daraktoci a kamfanin.
"Abu na biyu, lokacin da na bar African Petroleum, duk da shi ma ya bar wurin, ya gayyace ni daga Amurka na zo bansan dalili ba.
"Ya ce min don Allah ya na so mu yi aiki tare, in zama daraktan gudanarwa a kamfaninsa, ban ce masa ina neman aiki ba."

Kara karanta wannan

Tsumagiyar Tallafin Fetur Ta Bugi Gwamnoni, Ana Tunanin Rage Facakar Kudi

Gwamnan ya kara da cewa Dangote ya dauki nauyin komai na yakin neman zabensa ba tare da wani ya sa hannu ba.

Sule ya ce ba zai manta da halaccin da Dangote ya masa ba

Ya kara da cewa:

"Tsan-tsan soyayya, Aliko Dangote ya ce min ya ga alama zan iya zama gwamna a jihar Nasarawa kuma zai ba ni goyon baya in yi.
"Alhaji Aliko Dangote shi ya yi wannan, kusan shi kadai akan goyon baya da za a bani na neman zabe irin na gwamna."

Gwamna Sule ya ce da zai aurar da 'yarsa da ke aiki a kamfanin Dangote, musamman ya bar duk abinda ya ke yazo daurin auren a kauye kuma ya ce shi zai ba da auren.

Kafin fitowarsa takarar kujerar gwamna, Sule ya kasance ma’aikaci a kamfanin Dangote, inda ya kasance Manajan Darakta.

Sule yayi aiki a manyan kamfanoni a kasar, kama daga na kera karafuna zuwa kamfanonin man fetur da sauransu.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Yaudara Ce”, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili

"N8,000 Da Yawa" Gwamna Sule Ya Kare Tallafin Shugaba Tinubu

A wani labarin, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya kare kudin tallafi da Shugaba Tinubu ke shirin bayarwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a 21 ga watan Yuli.

Gwamnan ya ce wadannan kudade ba kadan ba ne idan aka yi la'akari da iyalai da ke fama da talauci a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel