Majalisar Dokokin Taraba Ta Amince Gwamna Kefas Ya Karbo Bashin Naira Biliyan 206

Majalisar Dokokin Taraba Ta Amince Gwamna Kefas Ya Karbo Bashin Naira Biliyan 206

  • Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya samu amincewar majalisa na karɓo rancen kuɗi sama da Naira biliyan 205
  • Majalisar dokokin jihar da ke Arewa maso Gabas ta amince da bukatar ciyo bashin ne a ƙarin kasafin shekarar 2023
  • Kefas ya ce zai yi amfani da waɗannan kudaɗe wajen gudanar da ayyunan more rayuwa, waɗanda zasu kawo ci gaba a Taraba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Taraba state - Majalisar dokokin jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta amince ta buƙatar ƙara ciyo bashin N206, 776,000,000.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa majalisar ta sahale wa gwamnan jihar, Dakta Agbu Kefas, ya runtumo wa jihar bashin kuɗi sama da Naira biliyan 206, wanda ya nema a karin kasafin 2023.

Zauren majalisar dokokin jihar Taraba.
Majalisar Dokokin Taraba Ta Amince Gwamna Kefas Ya Karbo Bashin N206bn Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Gwamna Kefas zai haɗo kan wannan bashi ne daga hannun bankunan kasuwanci huɗu domin aiwatar da ayyukan more rayuwa da ci gaba ga al'ummar Taraba.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Bankaɗo Badakalar N4bn Da Aka Wawure, Ta Cafke Uba da Ɗansa

Abinda ke ƙunshe a ƙarin kasafin kuɗin 2023?

Ƙarin kasafin kuɗin 2023 da gwamnan ya miƙa majalisar dokokin ya kunshi naira N10, 280, 679, 714 na kashe-kashen kuɗin yau da kullum da N196,495,320,285 na manyan ayyuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mambobin majalisar dokokin sun amince da ciyo bashin ne bayan samun saƙo daga mai girma gwamna, Agbu Kefas a hukumance.

A wata wasiƙa da ya aike wa majalisar, gwamna Kefas ya yi bayanin cewa bashin kuɗin na da lamunin shekara huɗu ƙafin a fara biya da kuma kuɗin ruwa kaso 18 cikin 100.

Ya kuma yi nuni cewa bankunan huɗu da za a karɓo rancen daga wurinsu, zasu cire kuɗinsu ne daga asusun bai ɗaya na tarayya (FAAAC), haɗakar kwamitin kasafta kudin shiga (JAAC)

Sai kuma asusun tattara harajin VAT da kuma asusun tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida, in ji gwamna Kefas, kamar yadda rahoton The Cable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Matawalle, El-Rufai Da Tsofaffin Gwamnonin 3 Da Sunayensu Ya Fito Cikin Ministocin Tinubu Kashi Na Biyu

Majalisa ta yi gyara a kasafin

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Mbamnga, Peter Diah, ya gabatar da kudirin cewa ya kamata a ware naira biliyan 5 don biyan kudaden gratuti na wadanda suka yi ritaya daga kananan hukumomi.

Nan take ‘yan majalisar ta amince da a shigar da su cikin daftarin karshe kafin tura wa gwamnan ya rattaɓa hannu.

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Amince da Nadin Kwamishinoni 18

A wani rahoton na daban Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tantance tare da tabbatar da naɗin sabbin kwamishinoni 18 da gwamna Dauda Lawal ya aiko mata.

Mambobin majalisar sun yi aikin tantance mutanen ne a zamansu na ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel