Arewa
Rahotanni sun nuna cewa wani abun fashewa da ake kyautata zaton bam ne ya tarwatsa a kasuwar shanu da ke garin Buni Yadi a jihar Yobe yau Jumu'a da tsakar rana.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta ba da umarnin korar shugaban yaki da cin hanci a jihar, Muhuyi Magaji Rimingado saboda saba umarnin kotu.
Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu ya soki kungiyar da ta yi barazanar masa kiranye inda ya ce ba zai bata lokacin wurin fahimtar da su ayyukan da yake yi ba.
Za a ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya mika sakon godiya ga Bola Tinubu kan samar da hukumar cigaban Arewa ta yamma (NWDC) domin farfado da yankin.
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya kori dukkan shugabannin riko na kananan hukumomi 21 a jihar yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a watan Agustan 2024.
Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kudurin dokar samar da hukumar raya yankin Arewa maso Yamma. NWDC ita ce irinta ta uku a Najeriya.
Cibiyar kididdiga ta NBS ta fitar da rahoto kan jihohi da yankuna da aka fi tsadar kayan abinci a Najeriya. Abia, Legas, Abuja, Gombe suna cikin jihoh masu tsada.
Hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana hakar ma'adanai da satar shanu cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas wajen yakar yan ta'adda.
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi martani ga Bello Matawalle inda ta tabbatar da cewa babu abin da zai saka ta zaman tattaunawa da 'yan bindiga saboda ba mafita ba ne.
Arewa
Samu kari