Arewa
'Yan gudun hijira a jihohin Niger da Borno sun roki Shugaba Bola Tinubu ya tausaya musu wurin dawo da Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu.
Mubakar Bello ya shiga gasar daukar lokaci mafi tsawo ana karatu a Guinness World Record. Malam MB zai rika rangada karatu zuwa safiyar Juma’a mai zuwa.
'Yan bindiga sun hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah a jihar Plateau mai suna Yakubu Muhammad a daren jiya Alhamis 18 ga watan Yulin 2024.
Kungiyar Ohanaeze ta kabilar Ibo ta umurci yan kabilar su nisanci zanga zanga a dukkan sassan Najeriya saboda kaucewa fadawa rikici da suka saba yi a baya.
Gwamnatin tarayya ta bayyana hotuna da bayanan fursunoni 69 da suka tsere daga gidan gyaran hali na Suleja a jihar Neja bayan makonni 11 da gudurwarsu.
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki, ta sanya ranar 1 ga Agusta domin yanke hukunci kan matashin da ake zargin ya kashe masallata a Kano.
Dan Gwamna Babagana Umara Zulum ya karyata zargin da ake masa na an tsare shi a kasar Indiya bisa laifin kashe wani dan kasar China a gidan rawa da daddare.
Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Malam Uba Sani, ta nisanta kanta da bidiyon cin zarafin da aka yi wa Dan Bilki Kwamanda. An zane shi da bulala.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana dalilin da ya sanya ake samun karuwar matsalar rashin tsaro a jihar. Gwamnan ya ce laifin ta'ammali da kwayoyi ne.
Arewa
Samu kari