Sanatan Kaduna Ya Shiga Matsala da Aka Yi Masa Barazanar ‘Kiranye’, Ya Roki Al’umma

Sanatan Kaduna Ya Shiga Matsala da Aka Yi Masa Barazanar ‘Kiranye’, Ya Roki Al’umma

  • Yayin da wata kungiya ta bukaci yin kiranye ga sanatan mazabar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Lawal Adamu ya mayar da martani
  • Sanatan ya caccaki kungiyar da ta yi wannan kira inda ya ce ba zai bata lokacin wurin fahimtar da su irin ayyukan da yake yi ba
  • Hakan ya biyo bayan kiranye da kungiyar Kaduna Peace and Tranquility Forum (KPTF) ta yi ga sanatan saboda rashin iya wakilci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman ya yi magana kan yi masa kiranye da wata kungiya ta yi.

Sanata Lawal Adamu ya caccaki kungiyar Kaduna Peace and Tranquility Forum (KPTF) kan barazanar da ta yi masa na kiranye.

Kara karanta wannan

A karon farko, Shugaba Tinubu ya yi magana kan matasa masu shirin yi masa zanga zanga

Sanata a Kaduna ya dauki zafi da aka masa barazanar kiranye
Sanata Lawal Adamu ya caccaki kungiyar da ta yi masa barazanar kiranye. Hoto: Sen. Lawal Adamu Usman.
Asali: Facebook

Kiranye: Sanatan Kaduna ya maida martani

Vanguard ta tattaro cewa kungiyar ta ba Sanatan wa'adin kwanaki 14 ne domin bayyana irin abubuwan cigaba da ya kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya yi martanin ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Segun Olatunji ya fitar.

Olatunji ya zargi kungiyar da neman yaudara da kuma yada bayanan karya ga 'yan mazabar Kaduna ta Tsakiya saboda biyan bukatar kansu.

"Kungiyar ta yi haka ne domin yaudarar jama'a da biyan bukatar kansu na siyasa da kuma wadanda suka dauki nauyinsu."
"Bai kamata mutanen Kaduna ta Tsakiya su yaudaru da wadannan maganganun kungiyar ba saboda rashin gaskiya da hujjoji."
"Muna kira ga mutanen Kaduna ta Tsakiya da sauran al'umma da su kwantar da hankalinsu tare da fatali da wannan barazana."

- Segun Olatunji

Sanatan Kaduna ya fadi kokarinsa a Majalisa

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 10 ayi zanga zanga, Tinubu ya dawo Najeriya bayan kammala taron AU

Lawal ya ce bata lokaci ne tunatar da kungiyar irin kwamitin da ya ke shugabanta da wadanda yake ciki da ke da matukar muhimmanci ga kasa.

Sanatan ya ce kwamitocin da yake ciki ba na malalatan 'yan siyasa ba ne kamar su da masu daukar nauyinsu wurin farfaganda.

Kungiya ta bukaci kiranye ga Hon. Jaji

Kun ji cewa wata kungiyar matasa a jihar Zamfara ta yi barazanar yin kiranye ga Hon. Aminu Sani Jaji saboda rashin katabus a Majalisa.

Kungiyar ta yi korafi kan rashin wakilci nagari daga Hon. Jaji wanda ke wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.