Jihar Adamawa
Allah ya yiwa wani aminin tsohon mataimin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Adamu Modibbo rasuwa bayan ya yi fama da ciwon sigakari a asibitin kwararru a Adamawa.
Ana binciken A. Yari da Amadu Fintiri a kan saba dokokin COVID-19 a Najeriya. Sabawa dokar COVID-19 zai iya jawowa Fintiri da Yari zama a kurkuku inji Gwamnati.
Gwamnatin jihar Adamawa karkashin jagoranccin Ahmadu Fintiri ta ware kwanaki uku domin alhinin mutuwar sarkin Bachama na jihar, Hama Bachama, Honest Stephen.
Matashiya mai shekaru 19 mai suna Lilian Benedict da ke gundumar Bwaranji a karamar hukumar Yola da ke Adamawa ta rasu a ranar Lahadi bayan haihuwar 'yan uku.
Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng na jihar Adamawa, Kama Lazarus Bakta a gidansa a safiyar yau Talata.
Rikicin kabilanci a tsakanin kabilar Lunguda da Waja ya yi sanadiyar rasa rayukan jama'a da dama tare da salwantar dukiya a jihar Adamawa, rikicin a kan gona ne
Gwamna Amadu Fintiti PDP ya tsoma baki a rigimar APC, ya fadi wanda zai yi nasara. Godwin Obaseki zai fafata da mutane biyar wajen samun tikitin APC a 2020.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira a ranar Alhamis ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta gina gidaje 500 don 'yan gudun hijira da ke jihohi hudu na arewaci.
APC ta bayyana cewa duk wani mamba nata da ya karbi mukamin siyasa daga hannun Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa wanda yake dan PDP ya sani cewa ya barta.
Jihar Adamawa
Samu kari