FG za ta gina wa 'yan gudun hijira gidaje 500 a jihohin Zamfara, Katsina, Borno da Adamawa

FG za ta gina wa 'yan gudun hijira gidaje 500 a jihohin Zamfara, Katsina, Borno da Adamawa

Hukumar kula da 'yan gudun hijira a ranar Alhamis ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta gina gidaje 500 don 'yan gudun hijira da ke jihohin Zamfara, Borno, Adamawa da Katsina.

Kwamishinan tarayya da ke kula da hukumar, Basheer Mohammed, ya sanar da hakan a garin Gusau yayin raba kayan tallafi ga 'yan gudun hijira a jihar.

Mohammed ya ce, gwamnatin tarayya ta matukar damuwa da halin da 'yan gudun hijira miliyan 2.4 ke ciki. Tana tunanin hanyar samar musu da matsuguni ta yadda za su yi rayuwa kamar kowa.

"Mun zo raba kayayyakin abinci da wadanda ba na abinci ba don amfanin jama'ar Anka, Gusau, Maradun, Shinkafi da Zurmi.

"A matsayinmu na cibiyar gwamnati, muna bada fifiko ne wurin bada kariya ga rayukan jama'ar da ke jihohi 36 har da babban birnin tarayya.

“Hukumar ta yi alkawarin gina gidaje 500 a jihohin Borno, Katsina, Adamawa da Zamfara a kashin farko na tallafin.

“Mun samu tabbaci daga jihohin Borno, Katsina da Adamawa cewa za mu samu hekta 50 ta fili.

"Hakan zai sa jama'a su koma garuruwansu sannan rayuwa ta koma kamar yadda take a da," yace.

Ya kara da cewa, hukumar ta dade da fara magana da masu zuba hannayen jari masu zaman kansu da na gwamnati don cimma manufarta.

FG za ta gina wa 'yan gudun hijira gidaje 500 a jihohin Zamfara, Katsina, Borno da Adamawa
FG za ta gina wa 'yan gudun hijira gidaje 500 a jihohin Zamfara, Katsina, Borno da Adamawa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Zamfara tana daga cikin jihohin da aka zaba don yin gidajen wanda hakan zai kara karfin guiwa ga gwamnatin ku da ta fara ginin Ruga.

"Kamar yadda na bayyana, abinda muka bai wa fifiko shine jama'ar da suka rasa gidajensu. Idan gwamnatin jihar Zamfara ta amince, za mu gina gidaje 500 cike da kayan bukata.

"Za mu samar da kayayyakin more rayuwa wanda ya hada da ruwan sha da cibiyoyin lafiya tare da samar da ayyukan yi ga jama'ar.

“Zan so amfani da wannan damar wurin karbar hekta 50 ta fili a wuri mai kyau. Amincewa tare da hadin guiwa da hukumar zai matukar ba wa masu zuba hannayen jari kwarin guiwa," Mohammed yace.

A yayin martani, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahadi Aliyu Gusau ya mika godaiya ga gwamnati a kan wannan jin kan.

Ya tabbatar da cewa an bai wa mutane da yawa kayan tallafi a jihar bayan ibtila'i ya fada musu.

Ya ce wannan kari ne a kan kokarin da gwamnatin Matawalle take yi, kuma suna goyon bayan gwamnatin tarayya a kan wannan aikin alherin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel