Rikicin kabilanci: Rayuka masu tarin yawa sun salwanta a Adamawa

Rikicin kabilanci: Rayuka masu tarin yawa sun salwanta a Adamawa

- Rikicin kabilanci a tsakanin kabilun Lafia da ke iyakar jihohin Adamawa da Gombe ya yi sanadiyar salwantar rayukan jama'a masu tarin yawa

- Kabilar Lunguda da Waja sun yi mummunan hargitsi wanda ya janyo zubda jini a cikin dare tare da asarar dukiyoyi masu tarin yawa

- An tattaro cewa rikicin ya barke ne sakamakon fada a kan gonaki

Mummunan hargitsi a tsakanin kabilun Lafia da ke iyakar jihohin Adamawa da Gombe ya kashe rayukan jama'a masu tarin yawa.

An kashe jama'a masu tarin yawa tare da halaka dabbobi da kuma salwantar dukiyoyi.

Rikicin kabilanci: Rayuka masu tarin yawa sun salwanta a Adamawa
Rikicin kabilanci: Rayuka masu tarin yawa sun salwanta a Adamawa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Lafiya gari ne da ke karamar hukumar Lamurde a jihar Adamawa.

An gano cewa rikicin ya barke ne sakamakon fada a kan gonaki.

Mataimakin gwamnan jihar, Crowther Seth ya ziyarci yankin inda ya samu rakiyar Birgediya kwamandan Yola, Birgediya Janar Sani Gambo Mohammed da sauran shugabannin tsaro.

Mataimakin gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta bankado wadanda suka yi aika-aikar. Ya kara da jan kunnen masu assasa rigimar.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Rundunar soji ta ragargaza 'yan ta'addan suna tsaka da taro

Rundunar 'yan sandan jihar a jiya ta ce ta damke mutum 32 da ake zargi da hannu cikin rigimar.

Tuni aka rufe wasu kananan hukumomi biyu a kan rikicin kabilancin.

A wani labarin kuma, mun ji cewa sakamakon ci gaban fadan kabilanci tsakanin kabilar Adara da Fulani a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, Daily Trust ta gano cewa an kashe matasa 4 'yan kabilar Adara a ranar Asabar.

'Yan uwansu ne suka konesu a kauyukan Doka sa Kallah da ke karamar hukumar Kajurun sakamakon zarginsu da suka yi da kaiwa Fulani bayanai a kansu.

An gano cewa, an banka wa Danladi Shekarau sa David Kampani wuta a kauyen Doka bayan an zargesu da yin fuska biyu yayin da aka kashe Jumare Anthony a kauyen Kallah duk a kan zargi daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel