Godwin Obaseki ne zai lashe tikitin Jam’iyyar APC a jihar Edo – Gwamna Fintiri

Godwin Obaseki ne zai lashe tikitin Jam’iyyar APC a jihar Edo – Gwamna Fintiri

Mai girma Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi magana a game da zaben jihar Edo, inda takwaransa, gwamna Godwin Obaseki yake fama da matsalar cikin gida.

Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin zabukan 2020 na kananan hukumomi na jam’iyyar PDP a jihar Edo ya ba gwamna Godwin Obaseki kwarin-gwiwa.

Ahmadu Umaru Fintiri ya na sa ran cewa Godwin Obaseki zai fita daga halin da ya samu kansa, kuma ya yi nasarar samun tikitin jam’iyyar APC har ya sake tsayawa neman tazarce a Edo.

Gwamnan Umaru Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida jim kadan bayan ya sauka filin jirgin sama da ke Benin, inda jam’iyyarsa ta PDP ta tura sa muhimmin aiki.

Gwamnan na Adamawa ya ji dadin yadda Obaseki ya amincewa PDP ta yi amfani da filin wasan Samuel Ogbemudia domin zaben ta, sannan kuma ya yi masa kyakkyawar tarba a Benin.

KU KARANTA: Takardun makaranta su na neman jawowa tazarcen Obaseki cikas

Godwin Obaseki ne zai lashe tikitin Jam’iyyar APC a jihar Edo – Gwamna Fintiri
Gwamna Amadu Fintiri Hoto: iDomiya
Asali: UGC

“Godwin Obaseki cikakken ‘dan siyasa ne; ya ba mu wurin taro, ba mu yi tunanin ba zai yi hakan ba. Zai kuma sauke ni a gidan gwamnati, wanda wannan ba bakon abu bane.” Inji Fintiri.

Umaru Fintiri ya kara da cewa: “Gwamna Obaseki zai fita daga cikin halin siyasar da ya burma a APC, ya hadu da ‘dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a zaben 19 ga watan Satumba.”

Fintiri ya na sa ran cewa ita ma PDP za ta fito da ‘dan takarar gwamna a zaben mai zuwa cikin kwanciyar hankali. Wannan ‘dan takara ne zai gwabza da wanda duk APC ta ba tuta a Edo.

“A matsayina na shugaban kwamitin PDP, za a ga gaskiya da adalci ga kowane ‘dan takarar da ya ke neman tikitin jam’iyya. Za mu tabbatar an yi yadda duk wanda ya yi allonsa zai wanke.”

A halin yanzu Godwin Obaseki zai fafata da mutum biyar wajen samun tutar APC. Kalubalen da zai fuskanta shi ne sabaninsa da tsohon gwamna kuma shugaban APC Adams Oshiomhole.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel