Gwamnan Fintiri ya kaddamar da aikin gadar sama ta N8.8 a jihar Adamawa

Gwamnan Fintiri ya kaddamar da aikin gadar sama ta N8.8 a jihar Adamawa

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa, Gwamnan Jihar Adamawa, Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, ya kaddamar da ginin titin gadar sama guda biyu da kuma titunan kasa a Yola, babban birnin jihar.

Da yake magana a yayin bikin kaddamar da kwangilar aikin, ya ce gwamnatinsa ta mai da hankali ne wajen tabbatar da biyan bukatun masu ababen hawa, tare da daukaka jihar zuwa matakin ci gaba.

Ya ce, “Wannan gagarumin aiki ne da zai kawo ci gaba a kokarin da mukeyi don ganin mun cika alkawarin da muka daukarwa al’ummar jihar Adamawa, a yayin yakin neman zaben kujerar shugabancin jihar.”

A cewar gwamnan, a yunkurin kara kwazon gwamnatinsa, wannan katafaren aiki zai lakume kudaden da sun kai kimanin naira biliyan 8.8 kuma sannan za su yi kokarin kammalasu a kan kari.

Gwamnan jihar Adamawa; Ahmadu Fintiri
Gwamnan jihar Adamawa; Ahmadu Fintiri
Asali: UGC

Yayin fafutika ta ganin ya cika alkawuran da ya daukarwa mutanen jihar Adamawa, Gwamna Fintiri ya shaida ce wa, gwamnatinsa tuni ta riga da fara ayyukan titinan a yankin Michika da kuma Madagali.

A wata sanarwa da Kwamishinan Ayyuka na jihar Adamawa, Alhaji Adamu Atiku ya fitar, ya ce ma'aikatarsa ta tsaya tsayin daka wajen bibiyar ayyukan, don ganin cewa an kammala su a lokacin da aka dauka.

Kwamishinan ya roki mazauna jihar da su ba wa gwamnati hadin kai wajen matsalar zirga zirga da ayyukan za su haifar.

KARANTA KUMA: 'Dalibai sun kauracewa makarantu yayin da aka koma a jihar Benuwe

Alhaji Atiku ya ce, “Ina kira ga jama’a da su karfafi wadannan ayyuka, lallai sai munyi hakuri da kalubalen da za a fuskanta yayin gudanar da wadannan ayyuka.”

Babban daraktan kamfanin Triacta Nigeriya Limited, Elie Abu-Farhat, ya ba da tabbaci a kan kwazon kamfanin, inda ya ce ayyukan za su kammalu cikin lokacin da aka dibar masa.

Ya ce, “Wannan gagarumin aiki da zai kawo ci gaba a jihar, za mu yi kokari don ganin mun cika alwashin da muka daukarwa al’ummar jihar Adamawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel