Gwamna Fintiri ya yi martani a kan zarginsa da kin kiyaye dokoki a filin jirgi
Gwamnatin jihar Adamawa ta musanta zargin da hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta kasa (FAAN) ta yi wa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri.
Hukmar FAAN ta zargesa da kin kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar korona a filin jirgin sama na Fatakwal a ranar Talata da ta gabata.
Darakta janar na yada labaran Fintiri, Solomon Kumangar, ya ce zargin da FAAN tayi mishi babu gaskiya a ciki saboda ba hakan bane ya faru a filin jirgin saman domin kuwa ya kiyaye dukkan dokokin da ake bukatar ya kiyaye.
Hadimin gwamnan ya ce Fintiri ya je Fatakwal ne don halartar taron a kan zaben jihar Edo tare da sauran gwamnonin PDP a wurin Gwamna Nyesom Wike.
Kumangar ya ce akwai abin mamaki da wannan lamarin ya zama wani abu daban ta mahangar gwamnatin tarayya. Sai dai idan kuma da wata manufa gwamnatin tayi hakan.
Ya kara da watsi da ikirarin FAAN inda tace gwamnan ya isa da tawagar mutum takwas. Ya ce mutum shida kacal ne suka bi gwamnan Fatakwal.
Mai magana da yawun gwamnan ya kalubalanci FAAN a kan ta bayyana bidiyon abinda ya faru a filin jirgin don jama'a su gani, Jaridar The Sun ta ruwaito.
"Ina mamakin yadda za a hada wa mutum karya ta yadda za a bata masa suna a matsayinsa na dan kasa nagari," yace.
"Gwamnan ya yi biyayya ga dukkan dokokin da aka bukacesa ya bi a yayin da ya isa filin jirgin amma mun yi mamakin rahoton da ya biyo baya.
"Hatta ma'aikatan FAAN da ke aiki a lokacin basu san cewa gwamna bane saboda yadda ya wuce ba tare da wani yunkurin daukar hankali ba.
"Wannan siyasa ce kawai da aka shirya don adawa. Ba za su rasa alaka da siyasar jihar Edo ba.
"Gwamnan ya je Fatakwal ne don taron PDP. A matsayinsa na mataimakin shugaban kamfen na Edo, ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron," Kumangar yace.
KU KARANTA KUMA: NDDC: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila
A ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, FAAN ta zargi Fintiri da kin bin dokar dakile yaduwar korona da gwamnatin tarayya ta sanar.
Ya ki amincewa a duba dumin jikinsa ko kuma ya tsaftace hannuwansa kamar yadda jami'an lafiya suka bukata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng