Bayan haihuwar 'yan uku, matashiya mai shekaru 19 ta riga mu gidan gaskiya

Bayan haihuwar 'yan uku, matashiya mai shekaru 19 ta riga mu gidan gaskiya

Matashiya mai shekaru 19 mai suna Lilian Benedict da ke gundumar Bwaranji a karamar hukumar Yola ta Kudu da ke Adamawa ta rasu a ranar Lahadi bayan haihuwar 'yan uku da tayi.

Josephine Geoffrey, mataimakiyar daraktar ayyukan jinya ta asibitin kwararru da ke Yola ta tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Talata a Yola.

Geoffrey ta ce matashiyar ta rasu ne sakamakon jinin da ta dinga zubarwa bayan haihuwar.

"Ta rasu ne sakamakon zubar da jinin da tayi bayan haihuwa amma 'yan ukun na nan cikin koshin lafiya.

"Talauci da rashin awon ciki da wuri ya taka rawar gani wurin mutuwarta.

"A don haka muke kira ga iyayen yara masu kananan shekaru da su dinga tisa keyarsu zuwa awon ciki idan sun fahimci suna dauke da juna biyu don gudun irin wannan," Geoffrey tace.

Mataimakiyar daraktar ta yi kira ga gwamnati, kungiyoyin taimakon kai da kai da kuma 'yan kasa na gari da su tallafawa jariran wurin samar musu da abinci tare da magunguna don rayuwa.

Kolostiki Benedict, mahaifiyar mamaciyar, ta ce mahaifin Lilian ya rasu a lokacin da take da shekaru takwas. Ta yi kira ga gwamnatin jihar Adamawa da ta tallafa wurin kula da jariran.

Taliba Kanakuru mai shekaru 26 shine saurayin mamaciyar, ya matukar razana da mutuwarta don ya ce ya kammala shirin aurensu bayan ta haihu.

Bayan haihuwar 'yan uku, matashiya mai shekaru 19 ta riga mu gidan gaskiya
Bayan haihuwar 'yan uku, matashiya mai shekaru 19 ta riga mu gidan gaskiya. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 25 a Zamfara

A wani labari na daban, wasu dalibai a kwallejin fasaha da ke Nekede a garin Owerri na jihar Imo sun mutu yayin gasar yin lalata.

Daliban, Cynthia Obieshi da Samuel Osuji sun mutu ne a ranar Lahadi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar, Orlando Okeokwu ya ce an kai gawarwakin daliban asibiti don ajiye wa a dakin adana gawarwaki.

Ya ce, "A ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni ta 2020 bayan samun rahoto jami'an 'yan sanda da ke Hedkwatan Rundunar da ke Nekede/Ihiagwa, sun tafi daki mai lamba 19, a Vic-Mic Lodge da ke JMJ Bus stop.

"Sun kutsa cikin dakin inda suka tsinci gawarwakin wata Cynthia Obieshi da Samuel Osuji.

"An gano cewa ita Cynthia ta ziyarci saurayinta, Samuel a ranar 13 ga watan Yunin 2020 inda ta kwana tare da shi amma da gari ya waye dukkansu ba su farka ba.

"Binciken da kwararru suka fara gudanarwa ya nuna akwai yiwuwar sun mutu ne sakamakon kwayoyi da suka sha.

"A halin yanzu dai an kai gawarwarkinsu dakin ajiyar gawa yayin da ake cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel