Ismail Sahagah ya zama sabon sarkin Bachama

Ismail Sahagah ya zama sabon sarkin Bachama

Dakta Daniel Ismaila Shagah ya zama sabon 'Hama Bachama', sarkin kabilar Bachama, a masarautar Bachama da ke jihar Adamawa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Humwashi Wonosikou, sakataren yada labaran gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya fitar ranar Laraba.

Ma su ruwa da tsaki a nada sabon sarki a masarautar Bachama sun zabi Shagah a matsayin sabon sarki bayan mutuwar tsohon sarki, Honest Irmiya, a watan da ya gabata.

"Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya amince da nadin Dakta Daniel Ismaila Shagah a matsayin sabon Hama Bachama biyo bayan mutuwar tsohon sarki Irmiya Stephen, sarki na 28 da ya mutu a watan jiya," a cewar jawabin.

Ismail Sahagah ya zama sabon sarkin Bachama
Atiku da tsohon sarkin Bachama
Asali: Twitter

Jawabin ya cigaba da cewa, "Gwamna Ahmadu Fintiri ya taya sabon Hama Bachama murna tare da yabawa ma su zaben sabon sarki wajen zaben Dakta Shagah ba tare cikin zaman lafiya da lumana."

DUBA WANNAN: Magance matsalar tsaro: Buhari ya bada umurnin yin garambawul a rundunonin tsaro

Finitiri ya bulaci sabon sarkin ya cigaba da aiyukan alheri da tsohon sarki ya faro tare da yin amfani da gogewarsa ta aiki wajen gina jama'arsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel