Mutuwar Hama Bachama: Gwamnatin Adamawa ta bada hutun kwanaki uku

Mutuwar Hama Bachama: Gwamnatin Adamawa ta bada hutun kwanaki uku

- Gwamna Ahmadu Fintiri ya bada hutun kwanaki uku na makokin mutuwar Hama Bachama, Honest Stephen, shugaban masarautar Bachama ta jihar

- Za a fara makokin daga ranar Litinin 29 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yulin 2020

- Basaraken ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi yana da shekaru 66 a duniya

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya bada hutun kwanaki uku na makokin mutuwar Hama Bachama, Honest Stephen, shugaban masarautar Bachama ta jihar.

Fintiri ya bada wannan umarnin ne a wata takardar da ya bada ta hannun sakataren yada labaransa, Humwashi Wonosikou, a ranar Litinin a garin Yola.

Kamar yadda takardar ta bayyana, za a fara makokin daga ranar Litinin 29 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yulin 2020.

Mutuwar Hama Bachama: Gwamnatin Adamawa ta bada hutun kwanaki uku
Mutuwar Hama Bachama: Gwamnatin Adamawa ta bada hutun kwanaki uku Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Daga yanzu, dukkan tutoci za su kasance a kwance a dukkan fadin jihar daga ranar Litinin 29 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli.

"Za a yi makokin ne don tunawa da rasuwar sarki Hama Bachama, Honest Stephen, wanda ya rasu a sa'o'in farko na ranar Lahadi a Numan," takardar ta ce.

Basaraken ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi yana da shekaru 66 a duniya.

Basaraken tsohon sojan Najeriya ne wanda yayi murabus.

KU KARANTA KUMA: Ku tsamo 'yan bindiga tare da karar da su - Masari ga rundunar soji

Ya gaji sarautar a 2012 bayan rasuwar Homun Asaph Zadok.

Marigayin basaraken ne na 28 a masarautar kuma an birneshi a ranar Lahadin a Lamurde, hedkwatar masarautar Bachama.

A wani labari na daban, mun ji cewa Florence Ajimobi, uwargidar marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ta yi musayar yawu da mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, kan mutuwar mijinta.

A wani bidiyo da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa an nuno mutanen biyu suna musayar kalamai a bainar jama’a a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni.

Jaridar ta yi bayanin cewa an yi musun ne a lokacin da wasu gwamnoni suka je yi mata ta’aziyya tare da iyalan Ajimobi.

A bidiyon, an gani Misis Ajimobi tana korafin cewa gwamnatin bata yi wa iyalan ta’aziyyar mutuwar mijinta ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel