Boko Haram ta halaka farar hula 223 da jami'an tsaro 89 a cikin wata 7

Boko Haram ta halaka farar hula 223 da jami'an tsaro 89 a cikin wata 7

Kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta kashe farar hula 223, sojoji 82 da 'yan sanda bakwai a cikin watanni bakwai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin, wanda ya auku tsakanin 2 ga watan Janairu zuwa 2 ga watan Augusta na wannan shekarar, ya faru ne a wurare daban-daban na jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Binciken ya nuna cewa, farar hula 21 da sojoji 13 sun jigata a cikin wannan lokacin.

Kusan makonni biyu da suka gabata, 'yan bindiga sun kai wa Gwamna Babagana Zulum hari a jihar Borno.

Lalacewar tsari a yankin arewa maso gabas ta sanya gwamnonin yankin suka zanta da shugaban kasa a jiya.

A taron, sun jaddada cewa 'yan ta'addan suna sake samun mambobi kuma akwai bukatar a yi wani abu don 'yan gudun hijira su koma gidajensu da gonakinsu.

A bangaren shugaban kasar, ya ce an samu nasarori masu tarin yawa a fannin tsaro amma dole ne shugabannin tsaro su kara kokari wurin tsaron kasar nan.

Boko Haram ta halaka farar hula 223 da jami'an tsaro 89 a cikin wata 7
Boko Haram ta halaka farar hula 223 da jami'an tsaro 89 a cikin wata 7 Hoto: Daily Post
Asali: UGC

A ranar 3 ga watan Janairun, an kashe farar hula uku a kauyen Bila-Ambokdar da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno, sojoji hudu da wasu 11 sun jigata a Jakana a ranar 4 ga watan Janairu a Borno.

'Yan sanda biyU sun samu miyagun raunika a ranar 6 ga watan Janairu a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu yayin da aka kashe wasu uku a wannan ranar a kauyen Kundori da ke Konduga a Borno.

A ranar 7 ga watan Janairu, an kashe farar hula 30 yayin da wasu 35 suka samu raunika a Gamboru da ke karamar hukumar Gamboru Ngala a Borno.

Sojoji takwas da farar hula takwas aka kashe a ranar 7 ga watan Janairu a karamar hukumar Monguno.

A ranar 10 ga wata, 'yan ta'adda sun kashe farar hula uku a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

A ranar 17 ga watan Janairu, sojoji biyar sub rasa rayukansu yayin da 'yan ta'adda hudu suka rasu a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

A ranar 18 ga watan Janairu, sojoji hudu sun mutu a kan titin Bama zuwa Gwoza a karamar hukumar Gamboru-Ngala yayin da sojoji 8 suka rasu a ranar 21 ga watan Janairu a Mainok.

An kashe fararen hula 23 a kauyen Lura da ke karamar hukumar Dikwa a ranar 23 ga watan Janairu yayin da wasu hudu suka mutu washegari a Muna Galti da ke karamar hukumar Jere.

A masallacin Bulabulin da ke Gwoza, farar hula uku sun rasu yayin da 13 suka jigata a ranar 25 ga watan Janairu.

Farar hula uku suna rasu a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri yayin da biyu suka jigata, sai sojoji biyi da aka kashe a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Sojoji uku sun rasu, wasu hudu sun jigata a ranar 4 ga watan Maris a Damboa. 'Yan sanda bakwai da farar hula daya sun rasu a garin Dapchi a ranar 5 ga watan Maris.

A ranar 21 ga watan Maris, sojoji 47 suka rasa rayukansu a kauyen Gorgi da ke Borno yayin da farar hula uku suka rasa ransu, wasu ukun suka jigata.

KU KARANTA KUMA: Ajali: Sauran sa'o'i kadan aurensa, ango ya yi mummunan hatsari

Farar hula bakwai sun rasu a ranar 13 ga watan Afirilu a kan titin Auno- Maiduguri-Damaturu, yayin da wani daya ya mutu a ranar 18 ga watan Afirilu a Buni Gari.

Farar hula 35 sun mutu a Usmanati Goni a ranar 13. Ga watan Yuni a Nganzai a Borno, yayin da farar hula 16 da sojoji tara suka rasu a babbar hanyar Damboa zuwa Maiduguri.

An kashe farar hula biyar a Moduri, Kalewa da Ngurori a ranar 21 ga watan Yuni a Magumeri da ke Borno, farar hula biyun mutu a Damasak a ranar 4 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel