Duk mamban da ya karba mukami daga PDP, ya bar jam'iyya - APC ta ja kunnen mambobinta
Jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta ce duk dan jam'iyyar da ya karbi mukami daga Gwamna Fintiri za a yi mishi korar kare daga jam'iyyar.
Gwamna Ahmadu Fintiri dan jam'iyyar PDP ne wanda cikin kwanakin nan ya nada masu bada shawara, hadimai na musamman tare da shugabannin cibiyoyi. A saboda haka ne gwamnan ya nada wasu daga cikin 'yan jam'iyyar APC.
Amma a wata takarda da jam'iyyar APC ta fitar a ranar Laraba da hannun sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mohammed Abdullahi, ya jaddada cewa duk mamban da ya karba wani mukami daga PDP za a kore shi daga jam'iyya.

Asali: UGC
Jam'iyyar ta ce, "Mun duba nade-naden da gwamnatin PDP tayi a jihar Adamawa amma mun hango sunayen wasu mambobin jam'iyyar mu.
"Muna son janyo hankalin 'yan jam'iyyar da aka nada a kan cewa duk wanda ya karba nadi daga wata jam'iyya da ba APC ba ya bar jam'iyyar.
"A yayin da muke jinjinawa 'yan jam'iyyar a kan gaskiyarsu da rikon amana yayin da suka yi watsi da nadin, duk wanda ya karba ha bar jam'iyyar mu gaba daya."
Jam'iyyar ta zargin gwamnatin da yunkurin hargitsa APC.
Ta ce, "A tsanake APC ke kallon kokarin jam'iyyar PDP na hargitsa hadin kan da ke APC. Wannan abun ba zai yuwu ba kuma har abada ba zai yuwu ba.
"A don haka muke kira ga 'ya'yan jam'iyyar mu da su mayar da hankali wajen goyon bayan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da muke fatan karbar mulkin Adamawa a 2023."
KU KARANTA KUMA: Covid-19: Jihohi 4 da suka yi watsi da umarnin FG na bude wuraren bauta
A wani labari na daban, mun ji cewa rikicin da ya barke a jam’iyyar APC ta reshen jihar Neja ya kai intaha bayan an kai ga cafke shugaban jam’iyyar mai-mulki.
Jaridar ta ce an kama Injiniya Mohammad Jubrin Imam a farkon makon nan, inda ake zarginsa da laifin cin kudin jam’iyyarsa.
Rahotanni sun ce kawo yanzu dai an saki shugaban. An cafke Jubrin Imam ne a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020.
An kuma sake shi ne a yau Laraba. Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Neja ya tabbatar da wannan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng