'Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukuma a Adamawa

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukuma a Adamawa

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng na jihar Adamawa.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun isa gidan Kama Lazarus Bakta sannan suka yi awon gaba da shi.

Masu garkuwa da mutanen sun isa gidan a sa'o'in farko na ranar Talata inda suka dinga harbi a iska kafin su samu shiga gidan.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce 'yan sanda da mafarauta tuni suka fara bin sahun masu garkuwa da mutanen don ceto sa.

"Zan iya tabbatar muku da cewa 'yan sanda tare da mafarauta sun bi sahun masu garkuwa da mutanen. Za mu yi iyakar kokarinmu don ganin mun ceto wanda aka sace tare da damke masu aika-aikar," yace.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukuma a Adamawa
'Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukuma a Adamawa Hoto: Punch
Asali: UGC

Mazauna yankin da suka tattauna da Daily Trust sun koka da yawaitar sace manyan mutane da ake yi a yankin.

KU KARANTA KUMA: Tuna baya: Abubuwa 12 da Oshiomhole ya fadi game da Obaseki a 2016

A gefe guda mun ji cewa dandazon jama’a a jihar Katsina sun fito domin yin zanga-zanga a kan hauhawan rashin tsaro a fadin jihar.

Masu zanga-zangar sun kawar da shingen da jami’an yan sanda suka sanya a manyan tituna yayin gudanar da tattakin nasu.

A wani sakon murya da majiyar Legit.ng ta samu, an jiyo daya daga cikin jagororin zanga-zangar mai suna Kwamrad Usman Hussaini Rafuka yana fadin cewa:

“Musababbin wannan zanga-zangar da muka shirya, kowa dai ya sani musamman indai mutum yana a yankin arewacin Najeriya, ya san menene musababbin.

“Musababbinta bai wuce yanayin yadda ake kisan al’umma, musamman idan kika dauki jihar Katsina, muna da kananan hukumomi kusan 15 wanda a kullun sai an zub da jini a wannan yankin.

“Da wuya ka ji an ce ba a kashe mutum 20 ba kai har mutum 100 ana kashewa a rana daya.

“Yanzu haka maganar da nake yi da safe akwai wanda yana daga cikin masu wannan zanga-zangar lumanan da muka shirya, wanda da safen nan na kira shi ya batun tafiya sai yake ce mun wallahi yanzu haka a jiya a Batsari akwai wani gari an shiga an tafi da kanin mahaifinsa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel