COVID-19: Gwamnatin Tarayya na binciken Yari da Gwamna Fintiri kan saba dokoki a filin jirgi

COVID-19: Gwamnatin Tarayya na binciken Yari da Gwamna Fintiri kan saba dokoki a filin jirgi

Ministan harkokin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika, ya ce gwamnatin tarayya ta na binciken sabawa matakan yaki da annobar COVID-19 a wasu filayen jirgin sama.

Jaridar Daily Trust ta ce ana zargin wasu manyan mutane da saba dokokin COVID-19 a filayen sauka da tashin jirgi uku da ke kasar nan.

Idan ta tabbata wadannan mutane sun saba doka, akwai yiwuwar gwamnati ta ci su tara ko kuma su yi zaman gidan yari na akalla watanni biyu, ko kuma a hada masu hukuncin biyu.

Da ya ke magana a birnin tarayya Abuja, Ministan ya bayyana cewa zaman kason da za a laftawa wadanda su ka saba doka a filayen jirgin saman zai iya kai tsawon shekaru goma.

Ministan ya yi wannan jawabi ne wajen zaman da kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar COVID-19 watau PTF ya yi da ‘yan jarida a garin Abuja a ranar Alhamis.

Hukumar FAAN ta kasa ta zargi gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari da kin bin sharudan da gwamnati ta sa.

Alhaji Abdulaziz Yari da Ahmadu Fintiri duk sun musanya wannan zargi mai nauyi da ke kansa.

KU KARANTA: Buhari ba zai iya karasa manyan ayyukan da ya kinkimo ba

COVID-19: Gwamnatin Tarayya na binciken Yari da Gwamna Fintiri kan saba dokoki a filin jirgi
Alhaji Abdulaziz Yari
Asali: Depositphotos

Sanata Hadi Sirika ya ce idan bincike ya nuna Ahmadu Fintiri da Abdulaziz Yari ba su aikata laifin da ake zarginsu da su ba, hukumar FAAN za ta fito gaban Duniya ta nemi afuwarsu.

“Zargin fasinjoji da su ka sabawa doka sun hada da tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari wanda na yi magana da shi jiya (Laraba) na tsawon lokaci da kuma gwamnan Adamawa mai-ci, Ahmadu Fintiri.”

Sirika ya ke cewa “Abdulaziz Yari ya na kan hanyarsa ta zuwa Kano ne a ranar Asabar.”

“Shi kuma Fintiri ya na Fatakwal da kuma Cif Nduka Obaigbena wanda ya zo Abuja.”

Abin da doka ta ce shi ne idan fasinja ya yi abin da ba daidai ba, za a daure shin a akalla watanni biyu. “Hukuncin zai iya zama daurin shekaru goma.”

“Idan mu ka kama babban mutum ya saba doka, abin da za mu yi masa cikin sauki shi ne mu tura shi wajen ‘yan sanda, wanda dole su gurfanar da shi, kuma daurin ba zai zama kasa da watanni biyu ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel