Allah ya yiwa na hannun daman Atiku, Adamu Modibbo rasuwa
- Allah ya yiwa wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Adamu Modibbo rasuwa
- Madibbo ya kasance aminin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
- Ya rasu yana da shekaru 63 a duniya bayan fama da ciwon sukari
Wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Adamu Modibbo, ya rasu a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli.
Madibbo wanda ya kasance aminin tsohon mataimakin shugaban kasa, ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.
Marigayi Madibbo ya taba neman takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) a 2003.
Daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) inda ya nemi tikitin jam’iyyar a 2019.
KU KARANTA KUMA: Yadda masu fyade suka kashe wata matashiya a jihar Neja

Asali: Original
Hadiminsa, Ahmed Jauro Katuka, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa marigayin ya rasu a asibitin kwararru a Yola.
Ya kuma bayyana cewar kafin mutuwar nasa ya yi fama da ciwon siga mai tsanani.
Moddibo ya rasu ya bar matan aure biyu da yara tara. Za a yi jana’izarsa daidai da koyarwar addinin Islama.
KU KARANTA KUMA: Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, ya fadi 'warwas' a gaban kwamiti
Marigayin wanda ya kasance lauya kuma ma’aikacin banki, ya yi aiki tare da bankin First Bank Plc kafin daga baya ya zama manajan darakta na Sigma Pension Ltd.
Ya kasance a cikin shugabannin kamfanoni da dama, ciki harda Adamawa Beverages Ltd, wadanda suke ruwan Faro.
A wani labari na daban, mun ji cewa Geoffrey Onyeama, ministan harkokin wajen Najeriya, ya kamu da cutar korona.
Onyeama ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli, cewa yana kan hanyarsa ta zuwa cibiyar killacewa.
"Na yi gwajin cutar korona karo na hudu a jiya bayan alamun ciwon makogwaro, sai dai kuma abun bakin ciki shine ya bayyana ina dauke da cutar a wannan karon.
"Wannan ita ce rayuwa, ka yi nasara a nan, ka fadi a can. Ina hanyar zuwa cibiyar killacewa kuma ina addu'ar dacewa da mafificin alkhairi," ya wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng