'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da 'yan fashi 43 a Adamawa

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da 'yan fashi 43 a Adamawa

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta kama gaggan 'yan fashi da makami 10 da masu garkuwa da mutane 33 a yankuna daban-daban na jihar.

Haka zalika rundunar 'yan sandan ta samu nasarar cafke wasu mutum 16 masu tayar da zaune tsaye da ake zargi da haddasa rikicin kabilu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Olugbenga Adeyanju, kwamishinan 'yan sanda na jihar, shi ne ya sanar da haka a taron manema labarai da aka yi ranar Litinin a garin Yola, babban birnin jihar.

Mista Adeyanju ya ce, an kama ababen zargin ne daga ranar 1 ga Yuli, kawo yanzu, sakamakon kokarin da jami'an 'yan sanda ke ci gaba da yi.

Gaggan 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane
Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Gaggan 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

Ya ce: "Rundunar 'yan sandan ta cafke masu garkuwa da mutane 33, 'yan kungiyar asiri 2, 'yan fashi da makami 10 da kuma mutum 16 masu haddasa husuma ta kabilanci a jihar."

"An samu nasarorin ne sakamakon fafutikar da jami'an tsaro suka yi wajen kwantar da tarzoma tare da samun goyon baya daga kwararrun mafarauta, gwamnati da mutanen jihar."

"Mun kama muggan makamai da suka hada da manyan bindigogi guda ciki har da kirar AK47 guda 5.

"Sauran makaman sun hada da alburusai 328, sassan jikin dan Adam, mota kirar Toyota mai dauke da lambar RBH 186 AA, babur mai kafa uku da kuma tsabar kudi har naira 58,420."

KARANTA KUMA: Buhari ya aikawa Sarki Salman sako na fatan samun sauki

Kwamishinan ya ce ababen zargin sun shiga hannu ne a wasu kananan hukumomin jihar da suka hada Fufore, Maiha, Gombi, Mubi ta Arewa da Yola ta Arewa.

Ya ce mutane 16 da aka kama bisa zargin haddasa rikicin kabilanci an kama su da muggan makamai dangane kuma suna da hannu a rikicin baya-bayan nan tsakanin kabilun Lunguda da Waja a karamar hukumar Guyuk da Lamurde.

A wani rahoto na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Hankula sun tashi a harabar Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Ogun, TRACE, a ranar Litinin bayan wani mutum, Fatai Salami ya kashe kansa a harabar hukumar.

A cewar rahotanni, Jami'an TRACE sun kama direban Salami ne ranar Alhamis 16 ga watan Yuli a Abeokuta saboda ya saba dokokin dakile annobar cutar coronavirus a jihar.

An zargi cewa baya kiyaye dokar bayar da tazara a cikin motarsa kuma bai saka takunkumin rufe fuskarsa ba kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel