Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku

Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku

An samu tsananin cunkoso a kan babban titin Yola zuwa Gombe a ranar Litinin bayan sama da ma'aikata 400 na kamfanin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun fito zanga-zanga wacce ta sa suka toshe hanyar zuwa babban birnin.

Suna zanga-zangar ne sakamakon cin zarafin ma'aikata mata da 'yan India a kamfanin Adama Beverages Limited ke yi a garin Yola, jaridar The Guardian ta wallafa.

A kamfanin ake samar da ruwan sha na Faro da kuma ruwan Lemo. Mallakin tsohon mataimakin shugaban kasa ne, Alhaji Atiku Abubakar.

Ma'aikatan sun bayyana dauke da manyan takardu, inda suke zargin manajan daraktan kamfanin da lalata da ma'aikata mata rana tsaka da kuma korar 'yan Najeriya aiki inda yake maye gurbinsu da 'yan India.

Ma'aikatan sun yi kira ga ma'aikatar kwadago da ta gaggauta shiga lamarin sakamakon cin mutuncin da ma'aikata 'yan Najeriya ke fuskanta a kasar su ta gado daga wurin Francis Vazheparambbil.

Ma'aikatan suna dauke da fostoci masu rubutu kamar haka: "Dole ne 'yan India su tafi. Ba mu bukatar su. Mu ba bayi bane" da sauransu.

Sun jajanta yadda ake wa 'yan Najeriya a kamfanin tamkar zamanin siyar da bayi.

Kakakin masu zanga-zangar, Abdullahi Maigida Bello, wanda ya zanta da manema labarai a madadin sauran, ya ce "tun bayan da dan India ya zama manajan daraktan, suna saka mu aiki kamar bayi a kasarmu ba tare da wani albashin kirki ba.

Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku
Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku. Hoto daga The Guardian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsohon gwamna a Najeriya ya yi kaca-kaca da karuwarsa, 'yan sanda sun damkesu

"Wasu daga cikinmu suna aikin wucin gadi na shekaru 12 kenan. Abinda ake yi shine kora da dauka ba tare da biya ba.

"Da yawa daga cikin manyan ma'aikatan an koresu ba tare da biya ba kuma ana maye gurbinsu da 'yan kasar India. Ko a cikin annobar nan, 'yan kasarsu yake kawowa don maye gurbin 'yan Najeriya".

"Babban manajan daraktan ya yi nasarar kawo jama'a daga kauyensu amma 'yan Najeriya da suka fi wasu daga cikin ilimi da kwarewa an bar su a matsayin ma'aikatan kwangila," yace.

Ya kara da cewa, "hatta wasu ayyukan da ya kamata a bai wa kananan ma'aikata, an kwashe an bai wa wadanda basu da kwarewa."

Hakazalika, shugaban manyan ma'aikatan, Kwamared Puke Jackson, ya sanar da manema labarai cewa, ana basu takardun tuhuma a duk lokacin da suka yi taro a kan matsalolin da basu shafi aiki ba.

"Mun zo a matsayin kungiya inda muke rokon gwamnati ta saka baki. Wannan matsalar na ci gaba da faruwa tun bayan da 'yan kasar India suka katantane kamfanin.

"Ana ci gaba da sallamar 'yan Najeriya da suka fi su gogewa," yace.

A yayin da manema labarai suka tuntubi Francis, ya ki yin tsokaci a kai inda ya ce "ba ni da matsala da 'yan jaridar Najeriya, ba zan yi muku magana ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel