Abun Bakin Ciki
Wani mutum a sansanin yan gudun hijira da ke Mandarari a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno ya yanka wani makwabcinsa bisa zarginsa da ake yi yana da maita.
Wani kare a Amurka ya harbe wani mafarauci bayan da ya ajiye bindigarsa a mazaunin baya na motarsa. Karen ya dira kan bindigar ne inda ta saici ubangidansa.
An gano hoton gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a gaban gawar 'dansa yana yi masa addu’a kafin kais hi gidansa na gaskiya bayan Allah ya amshi ransa.
Wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun fille kan Chris Ohizu, shugaban karamar hukumar Ideato ta arewa a jihar Imo bayan sun karbi miliyan 6.
Rundunar yan sandan Kano ta tabbatar da kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da yi wa idon wata amarya lahani ana tsaka da bikinta. Za a gurfanar da su a kotu.
Wani matashi da azal ta hau kansa a jihar Delta ya doke mahaifiyarsa inda ta sheka lahira. An gano cewa wata kadarar gado suka siyar amma kason bai masa ba.
Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina–finan Najeriya ta Nollywood, Femi Ogunrombi wanda aka fi sani da Papa Ajasco, ya rasu. An samu labarin ne a yau.
Wasu masu shirin zama ma'aurata sun hadu da ajalinsu sakamakon sabon harin da yan bindiga suka kai karamar hukumar Ideato ta arewa a jihar Imo a ranar Talata.
Yan bindiga sun farmaki garin Sapele da ke jihar Delta inda suka kashe wani kansila na yankin Warri ta arewa, Bigha Grikpa, da wasu mutum uku a ranar Laraba.
Abun Bakin Ciki
Samu kari