Abun Al Ajabi
An yanke wa wani mutumin kasar Faransa hukuncin daurin shekara biyar a gidan kurkuku saboda samunsa da laifin harbe wani zakara saboda ya dame shi da cara.
Al'umman Folwoya Goriji da ke karamar hukumar Mayo Belwa na jihar Adamawa sun koka kan yadda suke cikin kangin rayuwa ba tare da samun tallafin gwamnati ba.
Wasu ma'auratan Najeriya sun zo da sabon salon yin hoton kafin aure, an dai gano saurayin da mai shirin zama amaryarsa kan kwangirin jirge sanye da Oksijin.
Wata yar kasar China mai suna Zhao mai shekara 31 da aka yi wa tiyatar sauya hanci ta yi matukar kaduwa bayan ta gano an gutsure mata kunne ba da izininta ba.
Wani dattijo mai shekaru 74 ya roki kotu da ta kwato masa kudi N50,000 da ya kashe wa wata budurwa yar shekaru 18, Rukaiyyat Idris bayan an hana shi aurenta.
Magidanci ya gudu ya bar matarsa da ke jego, Evelyn, a wani asibitin kudi da ke Okpoko, karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra, inda ta haifi 'yan uku.
Kamfanin motoci ta Kantanka karkashin jagorancin Shugaban kamfanonin Kantanka Group, ta kera wata sabuwar mota wanda wani matashi dan shekara 18 ya fara kerawa.
Wani bawan Allah ya shiga tsakanin wasu kaji guda biyu da ke fada, mutumin rike da kaji a dukka bangarorinsa biyu na hagu da dama yayinda yake yi masu nasiha.
Soyayya ruwan zuma dadi sannan idan ta baci ta fi madaci, hakan ce ta kasance ga likitan kasar Ghana, bayan bayyanar bidiyonsa yana ta rusa kuka kamar karamin.
Abun Al Ajabi
Samu kari